Jama’ar Zariya Sun Maka Rundunar Sojin Najeriya A Kotu

0
318

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

A ranar Laraba ne jama’ar yankin Gyallesu da ke karamar hukumar Zariya suka garzaya gaban wata babbar kotu mai daraja ta biyu don kai karar rundunar sojin Najeriya a kan kwace musu gonakinsu.

Sun kai karar shugaban rundunar sojin Najeriya, Yusuf Buratai, shugaban NMS Zaria, Mohammed Mukhtar-Bunza, Ministan tsaro, Bashir Magashi da ministan shari’a Abubakar Malami.

Majiyarmu ta bayyana cewa jama’ar yankin sun yanke hukuncin kai karar gaban kotu ne bayan da suka zargi cewa an kwace musu gonar da suka gada tun daga kaka da kakanninsu.

A zaman kotun da aka yi a yau Laraba, 29 ga watan Janairu, Mai shari’a Dabo ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 11 ga watan Maris.

A tattaunawar da aka yi da lauyan masu kare kansu, A. I. Omaji, ya ce sun bukaci a kara musu kwanaki kafin a fara shari’ar. Mai shari’a Dabo kuwa ya amince da hakan.

Lauyan masu kara ta bayyana cewa tuni kotu ta gindaya wa rundunar sojin Najeriya dokar hana karbar gonar daga jama’ar yankin Gyallesu din.

Rahotanni sun bayyana cewa an dade ana rigima a kan wannan gonar wacce jama’ar yankin Gyallesu din suka ce sun gaje ta ne daga kakanninsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here