Majalisa Ta Amince Da Nadin Sabon Shugaban Hukumar Alhazan Najeriya

0
308

Ka'aba

Rahoton Z A Sada

MAJALISAR dattawan Najeriya ta amince da nadin Zikrullah (Sikiru) Olakunle Hassan a matsayin sabon shugaban hukumar alhazai NAHCON.

Majalisar ta amince da nadin ne bayan karbar rahoton kwamitinta kan harkokin waje game da bukatar hakan da shugaba Muhammadu Buhari ya mika ta neman amincewa da nadin Zikrullah da sauran shugabannin hukumar.

A zamanta na ranar Alhamis, majalisar ta kuma amince da nadin Abdullahi Magaji Hardawa a matsayin babban kwamishinan hukumar.

Sauran manyan kwamishinonin hukumar su ne Nura Hassan Yakasai da Nura Abba Musa Rimi da Sheikh Momoh Suleman Imonikhe da Abba Jatois da Halima Jibril da Garba Umar da Ibrahim Ogbonnia Amah da sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here