Ya Kai Matarsa Kotu Bisa Zargin Lalata Da Wani

0
298
Rabo Haladu Daga Kaduna
WANI dan kasuwa mai suna David Ishaku a Abuja ya nemi wata kotun shari’ar gargajiya da ke zamanta a Nyanya ta raba aurensa da matarsa mai suna Lucia bayan ya kama ta suna lalata da wani mutum.
Mai korafin wanda ke zaune a unguwar Nyanya, ya kuma bayyana wa kotu cewa abokin lalatar nata ya kore shi daga gidansa, a cewar rahoton kamfanin dillancin labarai na NAN.
“Wata rana na yi tafiya ba tare da na fada wa matata ranar da zan dawo ba,” in ji David Ishaku.
Ya ci gaba da cewa: “Na dana wa mata tarko kuma ta fada. Na dawo daga tafiya na tarar ta kawo kwarto gida.
“Da na yi mata magana sai kwarton nata ya taya ta suka dake ni. Raina ya baci sosai kuma na ce mata ta bar mani gidana amma ta ki. Ta watso kayana waje kuma ta kolekofa.
Lokacin da aka karanto zargin da ake yi mata, Lucia ba ta cikin kotun sannnan kuma ba ta aika da dalilin da ya sa ba ta je ba, in ji NAN.
Da yake magana, mai Shari’a Shittu Mohammed ya ce: “Wannan ne karon farko da batun ke zuwa gaban kotu, kuma wadda ake zargin ba ta nan.
“Saboda haka bisa adalcin kotu, an dage wannan shari’a har zuwa 3 ga watan Fabarairu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here