Hakkinmu Ne Ba Al’umma Kulawa Kodayaushe A Asibitoci – Hukumar Tattara Bayanai

0
676

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

MA’AIKATAR Hukumar Tattara Bayanai da Adanawa na Asibitoci ta kasa, reshen Arewa ta Yamma da ke jihar Kaduna, ta bayyana cewa hukumarsu ce ke da alhakin kulawa da duk wasu majinyata ko marasa lafiya da ke bukatar kulawa a duk wasu asibitocin da ake ziyarta.

Shugaba mai kula da al’amuran sashen Arewa ta yammah Alhaji Umar Sani ne, ya bayyana hakan a garin Kaduna a yayin wata zantarwarsa da wakilinmu, inda ya yi ikrarin cewa ma’aikatar hukumarsu ce ke da hakkin kula da walwalar duk wasu majinyata da ke zuwa asibitoci.

Shugaban Umar, ya kara da cewa a duk lokacin da wasu majinyata suka ziyarci wata asibiti, ma’aikatan hukumarsu ne ke fara tarbarsu a matsayin jami’an hulda da jama’a domin tabbatar da kulawa da samun abin da wannan al’umma suka zo nema na lafiyarsu a cikin wannan asibitin cikin sauki.

A cewarsa, ma’aikatan hukumarsu ne mutanen dake fara yin hulda da duk wasu majinyata, kana su ne ke kare yin hulda da su ta hanyar bude masu fayel na bayanansu wanda daga bisani za su ba su wani dan kati wanda za su rika yin amfani da shi wajen samun damar yin wasu abubuwan da harkallan neman lafiyarsu a duk lokutan da suka zo a asibitin.

Ya ce ” ba aikin ma’aikatanmu bane bada kati kawai amma yana daya cikin aikinsu saboda duk maralafiyar daya shigo asibiti, inda zai fara zuwa shi ne nan wannan daki inda zai karbi kati, kuma hakkin su wadannan ma’aikatan ne su tarbi wannan maralafiyar, sannan su amshi bayanan shi a matsayinsu na jami’an hulda da jama’a.”

Umar ya ci gaba da cewa ma’aikatarsu ce ke da hakkin tantance duk wasu ma’aikatan da ake dauka don samun kwararru da za su gudanar da ayyuka a bisa tsari wanda hakan ya sanya suke yiwa duk wasu ma’aikata da daliban ilimin wannan sashen jarabawa ta karshe wanda su suke tsarawa domin tantance su kafin a dauke su aiki a duk wata ma’aikata ko asibiti.

A cewarsa, fa’idar wannan aikin tattara bayanan da adanawa wanda suke yi na da nasaba da samawa marasa lafiya wata damar samun bayanan da za su iya yin amfani da su a duk lokutan da ake bukata musamman wajen ganin wani likita wanda kila ba shi mutane suka gani ba a yayin zuwansu asibitin na farko.

Hakazalika, ya kara da cewa ma’aikatar hukumar tasu ce ke da alhakin sama wa mutane takardar mutuwa idan ana da bukata, kana da duk wasu bayanai na shaida wanda za a iya gabatar da ita a gaban duk wata hukuma idan an samu matsala da wani yana ganin an yi masa ba daidai ba har kai ga ya shigar da kara.

“Su kansu likitoci kamin su zama masu tuntuba, da wadannan bayanan suke amfani wajen yin binciki su, sannan wannan bayanan ne ake bai wa asibiti domin susan abin da ake bukata don su tanadar wa marasa lafiya kayayyakin da ya dace na kula da lafiyarsu, kana su kansu gwamnati da wadannan bayanan ne suke yin amfani wajen gudanar da duk wasu tsare-tsare su a asibitoci.”

“Mu cibiya ne mai tabbatar da ma’aikata sunyi abin da ya kamata domin mu ne muke hurar da ma’aikatan, sannan mune muke tantance duk wasu makarantu da suke ba da irin wannan ilimin kamin mu ba su izini da amincewa nayin aiki, haka kuma duk  lokaci zuwa lokaci mu kan ziyarci wurare mu ga ko suna da kayan aikin daya kamata da amfani da shi.”

“Hakkin hukumarmu ne, mu rika ziyartar asibitoci don mu ga yadda suke gudanar aiyukan wanda idan ta kama mu ba su shawarwari akan yadda za su tafiyar da al’amura, kana muna aiki da wadanda suka ba ma’aikatan hukumominmu aiki a cibiyoyin kiwon lafiya ko da a matakin kananan hukumomi ko na Jiha.” Inji shi

Shugaban mai kula da sashen Arewa ta yammah, ya shawarci jami’o’inmu da suyi kokarin sanga wannan sashe nasu na tattara bayana da adanawa a cikin harkar koyarwasu domin dalibai masu karatu a wannan sashen su samu karin ilimi mai inganci ta yadda za su samar damar gudanar da aiyukansu cikin sauki da kwarewa.

A karshe Shugaban Umar Sani, ya yi kira ga jama’a da su rika hakuri da jami’an su, kana su rika sanar da hukumarsu idan sun samu matsala da wani jami’ansu, domin samun damar warware matsalar cikin sauki a mutunce, saboda bai dace aji ana rikici tsakanin maralafiya ko mai jinya da duk wani ma’aikaci ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here