Neman Shugaba Buhari Da Ya Yi Murabus Shirme Ne – Garba Shehu

0
344

Rahoton Z A Sada

FADAR shugaban Najeriya ta Aso Rock ta ce kiran da Sanata Eninnaya Abaribe ya yi ga shugaba Buhari da ya yi murabus shirme ne.

Abaribe ya yi kiran ne gaban majalisar dattawa da nuna gwamnati ta gaza wajen daukar matakan tsare rayuka, da dukiyoyin al’umma, da ya hada da rashin sauya manyan hafsoshin rundunar sojan Najeriya bayan dadewa kan kujerunsu. A dalilin haka ya bukaci shugaba Buhari ko gwamnatin ta yi murabus.

Sanarwa daga mai taimaka wa shugaban kan labaru Garba Shehu ta ce ra’ayin na Abaribe shi kadai ya shafa, don ba ra’ayin al’ummar Najeriya ba ne. Kazalika, sanarwar ta caccaki Abaribe da yadda ya tsaya wa Shugaban ‘yan awaren Biyafara Nnamdi Kanu har ya arce daga Najeriya.

Domin haka fadar ta ce ba abun mamaki ba ne in dan adawa irin Abaribe ya furta irin wadannan kalaman don dama ya saba yin hakan.

A makon jiya shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN Rebaren Samson Ayokunle, ya nuna damuwa ga rashin sauya hafsoshin tsaron da ke cikin dalilan da ya ke ganin sun hana gamawa da ‘yan ta’adda.

Wani dan siyasar APC Umar Musa Gital na da ra’ayin rashin sauye-sauye a gwamnatin ta shugaba Buhari ka iya kawo cikas ga nasarar ta a 2023.

Zuwa yanzu dai gwamnatin ba ta ce komai ba kan kiran garambawul ga hafsoshin tsaron in ka debe bayanin da shugaba Buhari ya yi cewa za a iya cimma nasarar idan dukkan ‘yan kasa su ka jingine banbance-banbancensu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here