Sanata Wamakko Ya Dauki Nauyin Dalibai 10 Domin Karatu A Jami’ar Kasar Ghana

0
1166
Mustapha Imrana Abdullahi
A kokarin ganin an samu cikakkun injiniyoyin kerekeren kimiyya da fasaha yasa sanata Dakta Aliyu Magatakarda Wamakko daukar nauyin yara dalibai 10 domin yin karatu a jami’ar kerekeren kimiyya da ke kasar Ghana.
Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya dauki nauyin tura dalibai ne su 10 domin yin karatu a babbar makarantar kimiyya kerekere, Jami’ar samar da kwararrun injiniyoyi da ke garin Accra, Ghana su yi karatu a fagen samar da Injiniyoyi, harkar kerekere, harkokin kiwon lafiya da ilimin Akantoci duk baki daya.
 Wannan na kunshe ne a cikin wata takardar da mai taimakawa sanata Aliyu Magatakarda Wamakko a kan harkokin yada labarai Bashir Rabe Mani ya Sanyawa hannu aka rabawa manema labarai.
Takardar ta ci gaba da cewa wadanda suka amfana duk an ba su takardun daukarsu makarantun a ranar Juma’ar da ta gabata a lokacin wani taron  da aka yi a gidan Sanata Wamakko, da ke kan titin Sahabi Dange a unguwar Gawon Nama, a Sakkwato.
Daliban sun fito ne daga kananan hukumomin Sakkwato ta Arewa, Sakkwato ta Kudu, Gudu, Tangaza, Silame,Wamakko da Wurno.
Daliban za su yi karatu ne na tsakanin shekaru hudu zuwa biyar a kan harkokin ilimin injiniyan gyaran wutar lantarki da na’urorin wuta, ilimin Injiniyan Na’ura mai kwakwalwa, Kimiyyar tattara bayanai, ilimin Akanta da kuma ilimin harkar kiwon lafiya.
Da yake gabatar da jawabi a wurin taron Sanata Wamakko cewa ya yi wannan ci gaba ne na irin aikin da yake aiwatarwa don ganin talauci bai samu wurin zama ba a tsakanin al’ummar Sakkwato don haka yake ta kokarin bunkasa ilimin matakan Jihar.
Sanata Wamakko da ke wakiltar mazabar Sakkwato ta arewa, ya bayyana batun ilimi a matsayin wata kadara da za a iya barwa yan baya musamman ma matasa da za su kasance manyan gobe kuma shugabanni nan gaba.
Sanata Wamakko,  wanda ya samu wakilcin babban Sakatare kuma kwamishina a ma’aikatar kula da mohali, mai ritaya, Alhaji Muhammadu Bello Sifawa inda ya ce a yanzu haka ssnatan na daukar nauyin dalibai daruruwa da ke karatun NCE, Difiloma da masu karatun digiri da na sama da digirin a cikin Nijeriya Nijeriya wajen kasar.
Ya shawarci daliban da suka amfana da su zama jakadu nagari ga iyalansu, Jihar Sakkwato da Nijeriya da al’ummar musulmi baki daya.
Sanata Wamakko ya kuma yi kira ga daukacin masu hannu da shuni, kungiyoyi masu zaman kansu da kamfanoni da su yi koyi da irin wannan abin alkairin ta yadda za a ciyar da harkar ilimin Jihar da kasa baki daya gaba.
Wamakko ya kuma yi alkawarin ci gaba da yin irin wannan matukar yana raye.
Daraktan kula da harkokin mulki na Sanata Wamakko, Alhaji Almustapha Alkali, cewa ya yi an yi kyakkyawar shirin ganin daliban sun samu gudanar da karatun cikin kyakkyawar yanayi.
Alkali ya ci gaba da cewa shirin biyan kudin makarantarsu cikin lokaci, wurin kwanan, abincinsu, kudin alawus alawus da sauran abubuwan bukatun yau da kullum duk an kammala su baki daya.
Wanda ya yi magana da yawun iyayen daliban Alhaji Abba Isa, godiya ya yi ga Sanata Wamakko sakamakon irin wannan gagarumin tsarin inganta rayuwarsu da yayansu ya kuma yi kira ga sauran masu hannu da shi kan su yi koyi da abin da Sanata Wamakko ke yi.
Mai magana da yawun daliban kuma Mustapha Garba Bello daga karamar hukumar Gudu alkawari ya yi da cewa za su tsaya su fuskanci harkokin karatunsu domin ba marada kunya wanda yin hakan shi ne kamar godiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here