Babban Burina Shi Ne Na Rubuta Littafai Da Harshen Kahugu- Kwamared Joseph

  0
  543

  Isah Ahmed Daga Jos

  KWAMARED Joseph  Ma’aji  Hamza,  wani matashi ne dan kabilar Kahugu, da ke Karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna. Kuma a halin yanzu dalibi ne da ke karatun digiri a harshen Hausa, a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

  Bayan haka wannan matashi ya yi wani babban kokari, na kirkiro bakake da wasula na rubutun harshensu na kabilar Kahugu. A wannan tattauna da ya yi da wakilinmu, ya bayyana abin da ya karfafa masa gwiwar yin wannan aiki.

  Haka kuma ya bayyana mahimmancin rungumar harsunan kasa, maimakon rungumar harsunan kasashen waje. Ga yadda tattaunawar ta kasance:-

  GTK: Mene ne tarihin rayuwarka

  Kwamared Joseph: Ni dai an haifeni ne a Kauyen Kahugu, da ke Karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna,  shekaru 47 da suka gabata. Kuma ni dan qabilar Kahugu ne.

  Na yi makarantar Firamare a Dingin Kahugu, kuma na yi makarantar Sakandire a makarantar Sakandire ta kauyen Kono,  da ke a Karamar Hukumar Kauru a Jihar Kaduna. Na yi karatu a kwalegin ilmi ta Kafanchan, daga nan na tafi Jami’ar Ahamdu Bello da ke Zariya, inda a yanzu nake karatun digiri a harshen hausa.

  GTK: To maye ya karfafa maka gwiwar kirkiro rubutun bakake da wasula na  harshen kabilar Kahugu?

  Kwamared Joseph: Babban abin da ya karfafa mani gwiwar kirkiro ruubutun bakaken harshen  kabilar Kahugu shi ne tsoron abin da  wani Lauya  dan qasar Amerika, mai suna  Poul ya fada. Cewa akwai wasu yarurruka a duniya da za a nemesu a rasa  nan gaba, saboda masu magana da irin wadannan harsuna,  sun yarda su sun rungumi harsuna na biyu.

  Yanzu ko a nan Najeriya  akwai harsunan da dama da suka mutu, saboda wannan dalili. Ko a  Karamar Hukumar Lere  akwai wasu  harsuna irin su harshen  Sheni, tuni sun mutu saboda yadda masu shi, suka yi watsi da shi.

  Ganin haka ya sanya na sami karfin gwiwar kirkiro bakaken rubutun na harshen Kahugu. Domin kabilar Kahugu da sauran masu jin harshen su rika amfani da su, wajen rubuce rubuce don a barwa na baya tarihi da gado. A sami hanyar rubuce-rubuce na al’adu da wake wake da harkokin kasuwanci da rubuta littafai da dai sauransu.

  Bayan haka kuma na sami karfin gwiwar kirkiro bakaken  na harshen  Kahugu ne, saboda na sami fahimta a karatun harshen hausa da nake yi, a Jami’ar Ahamadu Bello.  Wanne ne ya dada karfafa mani gwiwar kirkiro wadannan bakake da wasula na wannan harshe na Kahugu. Domin bai kamata mu dogara da bakon harshe ba, mu bar namu ya mutu.

  GTK; Kamar yaya wadannan bakake da wasula na harshen Kahugu da ka kirkiro suke?

  Kwamared Joseph: To yadda wadannan bakake  da wasula na harshen Kahugu da na kirkiro  suke su ne bakaken guda 42 ne

  Manyan bakaken sune: B,  V,  C, D, X, F, G, GB, GH, GW, GY, H, J, K, Q, KH, KP, KW, KY, L, MP, N, N, N, P, PK, PY,  R,  R, S,  SH,  TS,  T,  W,  XY,  Y,  Y,? Z,

  Kananan bakaken sune b, v, c, d, x, f, g, gb, gh, gw, gy, h, j, k, q, kh, kp, kw, ky, l, m, mm, mp, n, n, n, pk, py, r, r, s, sh, ts, t, w, xy, y, y,? z

  Wasulan kuma  guda 18 ne.

  Manyan bakaken wasulan sune A, E, I, O, U, AA, EE, EL, II, OO, UU, AI, AU, OI, UI, IU, W, Y,

  Kananan bakaken wasulan sune: a,  e,  I,  o,  u,  aa, ee,  el,  ii,  oo,  uu, ai, au, oi, ui, iu, w, y,

  GTK: Wanne irin cigaba ne kake ganin wannan aiki da ka yi, zai kawo wa harshen kahugu da al’umma baki daya?

  Kwamared Joseph: Ci gaban da nake ganin wannan aiki zai kawo wa harshen Kahugu, shi ne al’ummar  kabilar Kahugu musamman matasa za su sami abin da za su rike na wannan harshe, ta yadda za su rika magana da  rubutu da shi. Haka kuma wannan aiki zai sanya sauran mutane wadanda ba sa jin wannan harshe, su koyi magana da wannan harshe, tare da rubutu da shi.

  GTK: A matsayinka na mai nazari kan harshe, wace irin gudunmawa ce kake ganin harsunan kasar nan, za su iya bayarwa wajen ci gaban kasar nan?

  Kwamared Joseph: Babu shakka idan ana son a cigaba a kasar nan, musamman ta fannin tattalin arziki dole, mu rungumi harsunanmu na kasar nan. Domin idan muka rungumi harsunanmu za a sami alfanu ta wajen rubuta littafai da habaka harsunan su rayu ta yadda ba za su bace ba a duniya.

  GTK: To nan wanne kira kake da shi zuwa ga al’ummarku na Kahugu, dangane da wannan aiki da ka sanya a gaba?

  Kwamared Joseph: Kirana ga al’ummar Kahugu shi ne su sani cewa wanda ya bar gida, gida ya bar shi. Don haka su bayar da goyan baya kan wannan aiki, domin mu bunkasa wannan harshe ta hanyar samar da rubuce rubucen adabi da littafai  da wannan harshe. Yin haka zai sanya wannan harshe ya yadu a duniya, kamar yadda manyan harsunanmu na Najeriya irin su  hausa da yarbanci da ibo suka yadu a duniya.

  GTK: Mene ne babban burinka kan wannan aiki da kayi?

  Kwamared Joseph: Babban burina shi ne na rubuta littafai da harshen Kahugu, domin mutanen Najeriya da duniya baki daya, su san da wannan harshe. Domin harshen da yake da rubutun bakake ana iya yin amfani da shi a ko’ina.

  GTK: Wanne kira ne kake da shi zuwa ga gwamnati dangane mahimmancin tallafawa wajen bunkasa harsunan kasar nan?

  Kwamared Joseph: Jan hankalina ga gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi da kamfanoni masu zaman kansu  shi ne su rika tallafawa wajen yin rubuce rubuce a harsunan kasar nan. Bai kamata mu rika dogara da harsunan kasashen waje ba, wajen nazarin harkokin kimiyya da kere kere da sauran harkokin yau da kullum ba. Ya kamata mu rika dogara da harsunanmu wajen yin wadannan abubuwa.

  Misali kamar kasar China sun rungumi harshensu, kuma yanzu a duniya babu wanda ya kai su cigaba saboda dogaro da harshensu da suka yi.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here