Dame Patience Da Aisha Buhari Sun Hada Kai Dalilin Maryam Babangida

0
438

Daga Usman Nasidi.

BA kasafai aka saba ganin matar tsohon shugaban kasa Jonathan, Dame Patience, da Aisha Buhari, uwargidan shugaban kasa, a zaune a karkashin rumfa guda daya ba idan aka yi la’akari da banbancin siyasa da ke tsakaninsu har yanzu.

Patience ta sha yin subutar baki tare da sukar
Buhari da kokarin kashe farin jininsa yayin da yake takarar kujerar shugaban kasa tare da mijinta a shekarar 2015.

Amma saboda taron tunawa da cikar shekaru goma da mutuwar Maryam Babangida, Aisha da Patience sun gaisa har ma sun zauna tare a wurin taron, wanda aka yi a Abuja.

Ana ganin cewa manyan gidajen biyu, da siyasa ta raba, sun fara sassauta zafin adawarsu tare da yin aiki tare. Ko a cikin watan da ya gabata sai da Jonathan ya kai wa Buhari wata takaitacciyar ziyara a fadarsa da ke Abuja.

Taron wanda Aisha, diyar IBB, ta shirya, ita kuma Aisha Buhari ta kasance mai masaukin baki, ya samu halartar Dolapo Osinbajo, Turai Yar’adua, Jastis Fati Lami Abubakar da sauran wasu manyan mata.

Maryam Babangida ta mutu ne a ranar 27 ga watan Disamba na shekarar 2009, bayan ta kamu da ciwon dajin mahaifa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here