Gwamnatin Amurka Za Ta Ba Najeriya Damar Karbo Kudadenta Na Sata Da Ke Kasarta

0
299

Rahoton Z A Sada

MINISTAN Shari’ar Najeriya Abubakar Malami, yana halartar wani taron hadin gwiwa na kwana uku tsakanin Najeriya da Amurka a birnin Washington, inda zai rattaba hannu kan wata yarjejeniya game da kudin gwamnatin da aka sace a Najeriya.

Bayanan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun ministan, Dokta Umar Jibrilu Gwandu, ya fitar ranar Lahadi a Abuja.

A madadin gwamnatin tarayyar Najeriya, ana sa ran ministan zai saka hannu kan wata yarjejeniya da yankin Island of New Jersey da kuma kasar Amurka kan kudaden sata da aka kai daga Najeriya.

Sanarwar ta ce kudaden sun kai dala miliyan 321 (kusan naira biliyan 116) a yunkurin gwamnatin Najeriya na dawo da kudaden da aka sace zuwa lalitar.

Ya kara da cewa taron na shekara-shekara ne tsakanin Najeriya da Amurka da nufin karfafa alakar difilomasiyya a tsakaninsu.

“Ministan ya ce wannan taro na musamman ne, wanda ba zai tabo wasu batutuwa da suka shafi al’amuran cikin gidan kasashen,” in ji sanarwar.

Baya ga minsitan shari’ar, akwai sauran wakilai daga Najeriya da suka hada da ministan kasuwanci Otunba Adeniyi Adebayo da ministan tsaro Manjo Janar Bashir Magashi (mai ritaya).

Sauran su ne Ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama, da mai bai wa shugaba Buhari shawara kan harkar tsaro Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya), da kuma ministar ma’aikatar jin kai da bayar da agajin gaggawa Sadiya Umar Faruk.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here