Dan Majalisa Shehu Bakauye Ya Raba Babura 100, Motoci 3

1
742
Mustapha Imrana Abdullahi
A kokarin ganin al’umma sun kwashi romon dimokuradiyya dan majalisar wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Giwa da Birnin Gwari Alhaji Shehu Bakauye ya raba wa jama’a Babura 100 da Motoci 3 kirar 406 domin inganta harkokinsu na yau da kullum.
A wajen wani babban taron da aka yi a karamar hukumar Giwa Honarabul Shehu Bakauye ya ce da yardar Allah sannu a hankali jama’a za su amfana da ribar dimokuradiyya don haka a ci gaba da yi masu addu’o’in samun nasara.
Ya kuma yi godiya fa Gwamnan Kaduna ubanshi mai rusau domin kawo ingantaccen gyara, ya kuma mika cikakkiyar godiyarsa ga shugabannin jam’iyyar APC na mazabarsa da suka zabe shi tun farko domin ya wakilce su.
An dai fayyace cewa mutane 50 ne za su amfana da Baburan a karamar hukumar Giwa kuma 50 a Birnin Gwari sai kuma motoci 2 a karamar hukumar ta Birnin Gwari yayin da za a amfana da mota daya a karamar hukumarsa ta Giwa.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here