Gwamnan Ondo Ya Nemi Buhari Ya Samar Da Dokar Halasta Tabar Wiwi

0
696

Daga Usman Nasidi.

GWAMNAN jahar Ondo, Rotimi Akeredolu ya yi kira ga gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari da ta kirkiro dokoki da za su halasta ta’ammali da tabar wiwi a Najeriya.

Gwamna Rotimi ya bayyana haka ne yayin ziyarar da ya kai fadar gwamnatin Najeriya, Aso Rock Villa a ranar Talata, 4 ga watan Feburairu inda ya yi ganawar sirri da shugaban kasa Buhari a ofishinsa, inda ya ce jaharsa za ta zuba hannun jari don hada magungunan kwayoyi daga tabar wiwi.

Da yake zantawa da manema labaru bayan kammala ganawarsa da Buhari, Gwamnan ya ce makasudin ziyarar daya kai ma shugaba Buhari shi ne domin ya gayyace shi zuwa garin Akure don ya kaddamar da gadar sama a Ore da ya gina a kan kudi naira biliyan 5, da kuma cibiyar masana’antu na jahar Ondo.

Gwamnan ya kara da cewa Buhari zai kaddamar da wadannan ayyuka ne don taya shi murnar cika shekaru uku a kujerar Gwamnan. Hakazalika gwamnan ya tabbatar da cewa tuni ya fara biyan N33,000 a matsayin karancin albashi ga ma’aikata.

“Ma’aikatan jahar Ondo sun fi kowa jin dadi a kasar nan saboda suna samun albshinsu a kan lokaci, kuma tuni muka fara aiwatar da sabon tsarin karancin albashi. Dalilin da yasa ban goyi bayan kungiyar tsaro ta Amotekun ba shi ne saboda bana bukatar wannan kafin jama’a su sake zabana a karo na biyu.” Inji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here