Masarautar Fika Ta Shirya Gangamin Fadakarwa Kan Cutar Zazzabin Lassa

0
424
Shugaban sarakunan Arewa, Sarkin musulmi
Muhammad Sani Gazas Chinade, Daga Damaturu
MASARAUTAR Fika karkashin Mai Martaba Sarkin Fika kuma shugaban majalisar sarakunan jihar Yobe, Alhaji (Dr) Muhammad Ibn Abali Muhammad Idrissa, ta shirya taron gangami tare da wayar da kan jama’ar masarautar ta hanyar tattaro ilahirin masu fada a ji a cikin al’umma, don tatrauna abubuwan da ke haifar da cutar masassarar Lassa domin da daukar matakin kariya.
Da yake kaddamar da jawabi a taron, Mai Martaba Sarkin Fika, wanda Galadiman Fika, Air Commodore Ibrahim Alkali (mai ritaya) ya wakilta, ya bayyana cewa zazzabin Lassa hattsabibiyar cuta ce wadda ke halaka jama’a farat daya.
Don haka ne basaraken ya bukaci mahalarta taron da cewa su isar wa sauran al’ummar masarautar sakon da taron ya tattauna kan sha’anin wannan cuta tare da gaggauta bayar da rahoton duk wani motsi mai alaka da cutar zuwa ga cibiyar kiwon lafiya mafi kusa da su.
Ya kara da cewa a  matsayin ku na shugabannin addini a cikin al’umma, ku ci gaba da gudanar da fadakarwa tare da wayar da kan al’umma a masallatai da coci-coci, tare da shaida wa jama’a su kula da tsabtace muhallan su, kana su kasance masu kula da tsabata a cikin kowane yanayi.
Da ya ke jawabi babban jami’in kula da kiwon lafiya a matakin farko (Primary Health Care Coordinator) a karamar hukumar Potiskum, a jihar Yobe, Abdulrahman Musa ya yaba dangane da yunkurin mai martaba  Sarkin Fika, wanda ya yi kira da muhimman matakan da za su taimaka wajen riga-kafin kamuwa da cutar zazzabin na Lassa.

Haka nan, su ma wakilan kungiyar kula da kiwon lafiya ta duniya (WHO), a karamar hukumar Potiskum, Usman Sunusi Bakabe, da takwaransa a karamar hukumar Fika, Mustapha Hassan, sun gabatar da nasu bayanan dangane da illar wannan cuta ta zazzabin Lassa ga dan Adam da kuma yadda al’umma za ta guje mata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here