Mu Ke Da Hakkin Lura Da Tsara Aiyukan Tattara Bayanai A Sashen Lafiya – HRORBN

0
460

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

MA’AIKATAR Cibiyar hukumar Tattara bayanai da adanawa ta kasa, ta bayyana cewa hukumar ce ke da alhakin tabbatar da lura da tsara duk wasu aiyuka wadanda suka danganci sashen tattara bayanai ta fannin sashen lafiya kana da bada lasisi ga duk wasu ma’aikatu da makarantu ko daliban dake wannan sashen tattara bayanai na fannin kiwon lafiya.

Ita dai wannan hukumar dake daya daga cikin hukumomi goma sha uku da gwamnatin tarayya ta kirkiro a karkashin doka ta 39 na shekarar 1989, wata cibiya ce wacce ta ke aikin ta a karkashin ma’aikatar lafiya ta kasa, kuma wacce ke da ikon tabbatar da lura kana da hakkin tsara harkokin tattara bayanai da adanawa a fannin lafiya.

Da yake yin karin haske game da irin aiyukan da hukumar ta su ta ke yi, shugaba mai kula da shiyar Arewa ta yammah da ofishin ta ke garin kaduna, Malam Umar Sani ya bayyana cewa ma’aikatar tattara bayanan wata hukuma ce mai zaman kanta wacce ta ke da hakkin kula da tsara duk wasu aiyukan da suka shafi tattara bayanai a sashen kiwon lafiya a kasa baki daya.

Ya kara da cewa hukumar ta su ce ke da hakkin tabbatar an samu kwararru sashen wanda hakan ya sanya suke horar da ma’aikansu da kansu kana suke shirya jarabawa ta musamman na karshe ga duk wasu daliban wannan sashen bayan sun kammala jarabawarsu ta karshe a makarantun su sannan ta bada lasisi ga wanda ta tantance su.

Ya ce ” akwai jadawali na gurbin yin karatun ilimin wannan sashen wanda wasu makarantu da jami’o’i ke yi musamman a kudu, toh amma mu anan arewa ne abun bai yi kwari ba saboda rashin sani da wayewar kai a cikin al’amuran mutanen mu na nan arewa.”

Acewarsa, fa’idar wannan aikin tattara bayanan da adanawa wanda hukumarsu ke yi na da nasaba da samar da bayanai wanda zasu taimakawa gwamnati ko hukumomin asibitoci ayayin da ake fuskantar wata barazana ko ake da bukatar yin wata canji na samun ci gaba ko neman wata hanyar da za a warware wata damuwar da ta shafi sashen lafiya.

Hakazalika, yin hakan wata dama ce da za ta ba al’umma marasa lafiya wata damar samun bayanan da za su iya yin amfani dasu a duk lokutan da su ke bukata musamman wajen ganin wani likita wanda kila bashi bane mutamin da suka gani baya ayayin zuwansu asibitin na farko ko na karshe.

Umar, ya kara da cewa ma’aikatar hukumar ta su ce ke da alhakin samawa mutane takardar mutuwa idan ana da bukata, kana da duk wasu bayanai na sheda wanda za a iya gabatar da ita a gaban duk wata hukuma idan an samu matsala da wani yana ganin anyi masa ba dai-dai ba har kaiga ya shigar da kara.

“Su kansu likitoci kamin su zama masu tuntuba, da wadannan bayanan suke amfani wajen yin binciki su, sannan wannan bayanan ne ake baiwa asibiti domin susan abin da ake bukata don su tanadarwa marasa lafiya kayayyakin da ya dace na kula da lafiyarsu, kana su kansu gwamnati da wadannan bayanan ne suke yin amfani wajen gudanar da duk wasu tsare-tsare su a asibitoci.”

“Mu cibiya ne mai tabbatar da ma’aikata sunyi abin da ya kamata domin mune muke hurar da ma’aikatan, sannan mune muke tantance duk wasu makarantu da suke bada irin wannan ilimin kamin mu basu izini da amincewa nayin aiki, haka kuma duk  lokaci zuwa lokaci mu kan ziyarci wurare muga ko suna da kayan aikin daya kamata ayi da amfani dasu.”

“Hakkin hukumarmu ne, mu rika ziyartar asibitoci don muga yadda suke gudanar aiyukan wanda idan ta kama mu basu shawarwari akan yadda zasu tafiyar da al’amura, kana muna aiki da wadanda suka ba ma’aikatan hukumominmu aiki a cibiyoyin kiwon lafiya ko da a matakin kananan hukumomi ko na Jiha.” Inji shi

Shugaban mai kula da sashen Arewa ta yammah, ya shawarci jami’o’inmu da suyi kokarin sanga wannan sashe nasu na tattara bayana da adanawa a cikin harkar koyarwasu domin dalibai masu karatu a wannan sashen su samu karin ilimi mai inganci ta yadda za su samu damar gudanar da aiyukansu cikin sauki da kwarewa.

A karshe shugaban Umar Sani, ya yi kira ga jama’a da su rika hakuri da jami’an su, kana su rika sanar da hukumarsu idan sun samu matsala da wani jami’ansu, domin samun damar warware matsalar cikin sauki a mutunce, saboda bai dace aji ana rikici tsakanin mara lafiya ko mai jinya da duk wani ma’aikaci ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here