Shugaba Buhari Ya Nada Amokachi Jakadan Kwallon Najeriya

  0
  348

  Rahoton Z A Sada

  SHUGABA kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya nada tsohon dan wasan Super Eagles, Daniel Amokachi a matsayin jakadan kwallon kafar kasar.

  Mai bai wa shugaban kasa shawara a harkokin yada labarai, Garba Shehu ne ya sanar da hakan.

  Amokachi mamba daga cikin tawagar Super Eagles da ta lashe kofin Nahiyar Afirka a Tunisia a 1994, yana kuma daga cikin ‘yan wasan da suka lashe zinare a wasan kwallon kafa a Atlanta a 1996.

  Cikin nasarorin da ya samu a sana’arsa ta kwallon kafa musamman a Ingila, ya lashe FA Cup a Everto a 1995.

  Bayan da Amokachi ya yi ritaya daga buga tamaula ya horas da Nasarawa United da kuma Enyimba International ta Aba.

  Cikin aikin da zai yi na jakada, Amokachi zai taimakawa ma’aikatar matasa da wasanni ta Najeria wajen zakulo fitattun ‘yan wasa masu taso wa a shirin da kasar ke yi na bunkasa wasanni.

  Garba Shehu ya kara da cewar ”Amokachi zai zama abin koyi ga matasa maza da mata wajen rungumar sana’ar wasannin.”

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here