‘Yan Bindiga 250 Ne ‘Yan Sanda Suka Kashe A Samamen Dajin Birnin Gwari

0
984

Rahoton Z A Sada

Rundunar yan sandan Najeriya mai yaki da ‘yan fashi ta Operation Puff Adder ta kutsa wani sansanin kungiyar ‘yan bindiga ta Ansaru, inda ta kashe 250 daga cikinsu, a cewar rundunar.

An kai harin ne a dajin Kuduru da ke Birnin Gwari a jihar Kaduna a safiyar ranar Laraba tare da taimakon sojojin sama, kuma ta ce an harbi wani jrigin helikwafta a yayin samamen.

“Samamen, wanda aka kai shi tare da hadin gwiwar rundunar IRT da ta CTU da STS da SARS, ya biyo bayan wasu bayanan sirri ne game da katafaren sansanin na Ansaru,” in ji wata sanarwa da hedikwatar ‘yan sanda ta fitar a Abuja ranar Laraba.

Ta kara da cewa: “‘Yan bindigar sun harbi wani jirgin helikwaftan ‘yan sanda, sai dai matukansa sun nuna juriya da kwarewa wurin saukar da jirgin lafiya ba tare da wani rauni babba ba,

A ranar Talata an samu rahoton cewa barayin shanu sun kashe kimanin mutum 13 tare da kora shanun da ba a san yawansu ba a wasu kauyuka da ke jihohin Kaduna da Neja da kuma Zamfara.

A makon da ya gabata Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya shaida wa BBC cewa suna da masaniyar cewa ‘yan bindiga sun yi sansani a yankin Birnin Gwari.

Ya fadi haka ne yayin da yake amsa tambayoyin ‘yan jihar kan alkawurran da ya yi kafin zabe a wani shiri na musamman da BBC ta gudanar mai taken ‘A Fada A Cika’.

‘Yan bindiga masu garkuwa da mutane suna ci gaba da cin karensu babu babbaka a yankin, inda jami’an tsaro da kuma shugabannin al’umma ma ba su tsira ba daga hare-harensu.

Rundunar ‘yan sandan ta ce an dauke jirgin da aka kai wa harin daga sansanin soji na jihar Kaduna zuwa Abuja.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here