Sharri Ake Yi Wa Abacha, Ni Ma An Nemi In Yi Wa Buhari Kazafi – Almustapha

0
475

Daga Usman Nasidi.

MANJO Janar Hamza Al-Mustapha ya karyata zargin da ake jifan tsohon shugaban kasa, Janar Sani Abacha, da shi na cewa ya saci makudan dalolin kudi.

Hamza Al-Mustapha ya bayyana cewa a lokacin da Sani Abacha ya dare kan mulki, abin da Najeriya ta mallaka a asusun kudin kasar waje bai da yawa.

A cewar Al-Mustapha, Abacha ya gaji abin da bai kai Dala miliyan 200 ne a asusun kudin kasar waje, amma kafin ya bar mulki ya tara dala tara da ‘yan kai.

Tsohon babban jami’in da ke kula da tsaron Sani Abacha a lokacin da yake kan mulki ya ce shugabannin da aka yi a baya ne suka sace dukiyar Najeriya.

Tsohon sojan ya yi wannan bayani ne a lokacin da aka yi hirarsa  da kafar yada labarai a safiyar Ranar Alhamis, 6 ga Watan Fubrairun 2020. Abacha ya bar $9.7b a asusun kudin kasar waje inji Al-Mustapha.

Hamza Al-Mustapha wanda ya yi zaman gidan yari na shekara da shekaru, ya ce an bukaci ya yi wa Muhammadu Buhari irin wannan kazafi da ake yi wa Abacha.

Al-Mustapha ya ce a baya an tursasa masa ya fito ya ce an saci kudin gwamnati a ma’aikatar PTF ta rarar mai da Buhari ya jagoranta a lokacin gwamnatin sojin.

A nasa ra’ayin, da za a fito a yi yaki da rashin gaskiya da gaske, da an kama mutane da yawa an daure a Najeriya. Al-Mustapha ya ce ba da gaske ake yin lamarin ba.

Kwanan nan muka ji cewa kasar Amurka za ta dawo wa gwamnatin Najeriya da wasu fam Dala Miliyan 308 da aka ce an wawura a lokacin Janar Sani Abacha.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here