An Tsinci Gawar Saurayi Da Budurwa A Dakin Janerato A Unguwar Badawa A Kano

0
527

Daga Usman Nasidi.

WANI mutum mai suna Auwallu Abdullahi mai shekaru 25 da budurwasa mai shekaru 19 an tsinci gawarsu a dakin janareto a Unguwar Gaya da ke yankin Badawa a cikin birnin Kano.

Ana zargin masoyan biyu sun mutu ne sakamakon hayakin janareton bayan sun kulle kansu a dakin Janareton na dogon lokaci. Lamarin ya faru ne wajen karfe 9 na dare a ranar Laraba.

Wata majiya, ta bayyana cewa wata matar aure ce ta gano gawawwakin a dakin Janareton da ke gidan.

An ce matar ta hanzarta sanar wa ‘yan sanda wadanda suka hanzarta mika masoyan asibitin kwararru na Murtala Mohammed da ke Kano inda aka tabbatar da mutuwarsu.

A yayin tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce hukumar sun samu labarin ne wajen karfe 9:30 na daren Laraba. Ya ce jami’an sun hanzarta zuwa wajen inda suka kwashesu zuwa asibitin kwararru na Murtala. A nan ne aka tabbatar da mutuwar dukkansu biyun.

Ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Habu A. Sani, ya ba da umurnin tsananta bincike don gano yadda wannan abin mamakin ya faru.

Wata majiya wacce ba mai karfi ba ta tabbatar da cewa Auwallu Abdullahi da budurwarsa na kokarin yin aure ne kafin aukuwar mummunan lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here