Ban Taba Zargin Buhari Da El-Rufai Da Kirkiro Kungiyar Boko Haram Ba – Ribadu

0
296

Daga Usman Nasidi.

TSOHON shugaban hukumar yaki da rashawa da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ya bayyana cewa sharri, karya da kage ake masa da ake yayata cewa wai ya zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamna Nasir El-Rufai da zargin su suka kirkiro kungiyar Boko Haram.

Ribadu ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Alhamis, 6 ga watan Fabrairu, sanarwar da ta samu sa hannunsa da kansa, inda ya yi kira ga hukumomin tsaro da su gudanar da bincike tare da kamo wadanda suka kitsa wannan magana.

Ya ce “Da misalin wannan lokaci na shekarar da ta gabata wani sako ya yi ta yawo da ake ikirarin daga wajena ya fito, sakon yana cewa wai na fallasa yadda aka kirkiri kungiyoyin ‘yan bindiga a sassan kasar nan.

“Da fari na yi watsi da batun saboda na dauke shi a matsayin cin fuska saboda a tunanina babu wani mai hankali da zai yarda da shi, amma sakon ya yi ta ruruwa, hakan tasa a ranar 17 ga watan Yuli na shekarar 2019 na musanta shi a shafina na Twitter.

“Amma abin haushi, bayan watanni shi da musanta sakon, mutanen da suka kirkiro sakon sun cigaba da watsa shi domin kawo matsala a cikin al’umma, don haka ina kara jaddada cewa ban taba furta wadannan kalamai ba, ban san wani abu game da abin da sakon ya kunsa ba, don haka jama’a su yi watsi da shi.” Inji shi.

Daga karshe Ribadu ya yi kira ga hukumomin tsaron da abin ya shafa da su gudanar da bincike a kan asalin sakon tare da kamo duk masu hannu a ciki saboda a cewarsa duk masu watsa labarun karya, musamman wanda zai kawo tashin hankali a al’umma, bai kamata a kyale su ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here