Kundin Tsarin Mulki Ya Hana Ni Tsoma Baki A Rikicin Gwamna Da Sarkin Kano – Buhari

0
568

Rahoton Z A Sada

SHUGABAN kasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana dalilan da suka sanya shi kin tsoma baki a rikicin Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.

Gwamna Ganduje da Sarki Sanusi II sun kwashe tsawon lokaci suna tafka rikici, lamarin da ya kai ga raba masarautar Kano zuwa masarautu biyar wadanda suka hada da sarautar Rano da Karaye da Bichi da Gaya, baya ga sarautar cikin kwaryar Kano ta Sarki Sanusi II.

Wannan lamari dai ya raba kawunan mazauna jihar har ta kai ga masu zaben Sarki a jihar sun kai gwamnatin Ganduje kotu kan batun.

Kazalika wasu kungiyoyin dattawan jihar da ma na arewacin Najeriya, da tsoffin shugabannin kasar sun sanya baki a cikin rikicin, wanda ya ki ci ya ki cinyewa.

Sai dai duk da tabarbarewar lamarin, shugaba Buhari bai fito fili ya tsoma baki ba, ko da yake wasu majiyoyi sun ce fadar shugaban kasar karkashin jagoracin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, ta rika kai gwauro tana kai mari kan batun

Amma wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta aike wa manema labarai ranar Juma’a, bayan shugaban ya gana da wata tawagar al’ummar Kano da ‘yan jam’iyyar APC wacce Gwamna Ganduje ya jagoranta zuwa wurin shugaban, ta bayyana dalilan da suka sanya shugaba Buhari bai tsoma baki kan rikicin ba.

Mai magana da yawun shugaban kasar, Malam Garba Shehu, ya ambato shugaba Buhari yana cewa: “Na san aikina a matsayina na shugaban Najeriya. Kundin tsarin mulkin Najeriya ya fayyace ayyukan Gwamnan jihar Kano, don haka da zarar aka ce batu yana gaban majalisar dokokin jiha (kamar yadda yake a can Kano) shugaban kasa ba shi da damar tsoma baki.”

Ya kara da cewa: “Na sha rantsuwar yin biyayya ga kundin tsarin mulki, kuma ba zan sauya matsayina ba.”

Da ma dai tawagar jihar Kano, kamar yadda Gwamna Ganduje ya shaida wa shugaban kasar, ta kai masa ziyara ne domin ‘nuna godiya’ saboda yadda yake mara wa jihar Kano baya ta hanyar samar da abubuwan more rayuwa da tsaro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here