Masu Garkuwa Da Mutane Sun Yi Awon Gaba Da Fasinjoji 9 A Kan Hanyar Abuja

0
507

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

WASU miyagun ‘yan bindiga sun tare babbar hanyar Lakwaja zuwa Abuja inda suka yi awon gaba da mutane cikin daji, daga cikinsu har da wani matashi dan bautar kasa mai suna Samuel Adigun.

Rahotonni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a daidai kauyen Idu a ranar Alhamis da ta gabata, kamar yadda wani mazaunin ya tabbatar, inda ya ce yan bindigan suna sanye da kakin Sojoji ne, kuma dauke da muggan makamai.

Matashi dan bautar kasa, Samuel yana gudanar da aikin yi wa kasa hidima ne a Abaji na babban birnin tarayya Abuja, kuma yana kan hanyarsa ta komawa garin Lakwaja daga Abaji ne lamarin ya rutsa da shi.

Majiyar ya bayyana cewa yan bindigan sun fito ne daga cikin daji , inda suka bude wa wata mota kirar Toyota wuta, suka samu tayoyinta, wanda hakan ya sa dole direban motar ya tsaya, ba tare da bata lokaci ba suka yi awon gaba da Samuel da fasinjoji 8.

“Ina cikin rafi ina wanke babur a lokacin da na ji karar harbe harbe, nan da nan na kwanta a kasa , har sai bayan da miyagun suka hau tsakiyar titi suka kwashe fasinjojin motar sa’annan na tashi na tsere.” Inji shi.

Shi ma wani babban jami’in hukumar NYSC ya tabbatar da sace Samuel, kuma ya ce tuni sun fara magana da ‘yan bindigan har ma an fara ciniki, inda yace suna sa ran za a sake su cikin ‘yan kwanakin nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here