Sun Soki Shugaba Buhari Kan Rikicin Ganduje Da Sarki Sanusi

0
300

Rahoton Z A Sada

KUNGIYAR dattijan arewacin Najeriya ta yi watsi da ikirarin shugaban kasar da ke cewa ba shi da ikon shiga tsakani a rikicin masarautar Kano tsakanin Gwamnan Abdulahi Umar Ganduje da Sarki Muhammadu Sanusi na II saboda tsarin mulkin Nijeriya ya yi masa iyaka.

Kungiyar ta ce a matsayin shugaban kasar na jagoran al’umma, ba daidai ba ne ya tsame kansa ya koma gefe lokacin da wani abu da ka iya barazana ga zaman lafiya da tsaron wani sashen kasar ya kunno kai ba. A cewarta yin hakan ba zai zama hawan kawara ga tsarin mulkin kasa ba.

Sai dai a martanin da ya mayar, shugaba Buhari ta hanyar mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu ya ce shugaban a matsayinsa wanda aka zaba kan tafarkin dimokuradiyya ya san huruminsa.

“Idan lamari yana gaban kotu ko majalisa, shugaba Buhari ba shi da hurumin sa baki, domin idan ya sa baki ya karya doka.

“Yana ganin gwamnatin Kano ita za ta magance duk wata matsala da ta taso da ke cikin huruminta,” in ji Garba Shehu.

Amma dattawan na arewa na ganin akwai abubuwa da dama da shugaba zai yi ba sai kundin mulki ya ce ya yi wanda ba zai sa ya karya kundin tsarin mulkin ba.

A cewar Dakta Hakeem Baba Ahmed, “bai dacewa ace kana babba kuma ka ga ana rikci ka ki sa baki, yana iya sa baki a rikicin Kano kuma akwai inda za a saurare shi a warware rikicin.” “Amma ka sa ido ka ce ba ruwanka, kuma kana matsayin shugaba akwai hakki,” in ji shi.

Ya kuma ce sun yi mamakin yadda shugaban ya nada wani kwamiti na daban duk da cewa su suka fara zuwa Kano a matsayin dattawan arewa da nufin sasanta rikicin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here