Yawan Yaran Da Ba Su Karatun Boko A Arewa Ya Na Damun A’isha Buhari

0
396

Daga Usman Nasidi.

UWARGIDAN shugaban kasa, Hajiya A’isha Muhammadu Buhari, ta ce yawan yaran da ba su zuwa makaranta a Yankin Arewacin Najeriya yana da ban takaici.

A’isha Buhari ta yi wannan bayani ne wajen kaddamar da wani shiri da kungiyarta wato Future Assured ta kawo domin bunkasa ilmi da koya sana’a a Najeriya.

Mai dakin shugaban Najeriyar ta kaddamar da wannan shiri ne a jihar Adamawa, inda za a samu kananan yara 750 da za a koya wa sana’a da kuma ba su ilmi.

Uwargidar shugaban kasa Buhari ta bayyana cewa akwai bukatar gwamnati ta yi wani abu cikin gaggawa game da wannan hali da ake ciki a Arewacin kasar.

“Mafi tada hankalin abin da ke faruwa shi ne a jihohin Arewa inda rikici da talauci suke kara jefa mutane cikin matsala game da rashin isassun kayan karatu.” Aisha Buhari ta ce an yi watsi da ilmin mata a Najeriya

Hajiya Buhari take cewa ana fama da rashin kayan aiki da wuraren daukar karatu, da kuma rashin isassun kwararrun Malaman, ban da matsalar albashi mai tsoka.

Abba Tahir ne wanda ya wakilci Uwargidar Najeriyar a wajen kaddamar da wannan shiri da dimbin jama’a za su amfana da wannan kungiya mai zaman kanta.

Dakta Abba Tahir shi ne mataimakin shugaban jami’ar Amurkan nan AUN, da ke Yola. A jawabinsa a madadin Buhari, ya yi kira da a dage wajen kai yara makaranta.

“Dole mu fahimci cewa sha’anin ci gaba da suna tafiya ne da ilmi. Sai mun koma mun gano ainihin silar matsalar ilmi, tattalin arziki, aikin gona da sauransu.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here