Al’ummar Bade a Jihar Yobe Sun Gudanar Da Bikin Kamun Kifi Na ”MAUYI GANGA”

0
1090

Muhammad Sani Gazas Chinade, Daga Damaturu

AL’UMMAR masarautar Bade a jihar Yobe sun gudanar da bikin al’adarsu da ake wa lakabi da MAUYI GANGA a wannan shekara ta 2020, wadda bikin shi ne na karo 38, da ya samu ya samu halartar Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni tare da shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmed Ibrahim Lawan hadi da manyan sarakuna da ‘yan siyasa da jami’an gwamnati da suka zo daga kowane lungu na kasar nan.

Wannan biki na kamun kifi da sauran wasannin gargajiyar al’ummar ta Bade dai an gudanar da shi ne a bakin kogin da akewa lakabi da Alkamaram dake gab da tsohon birnin Bade Gogaram mai dimbin tarihi ga kabilar tq Badawa.

Tarihin wannan biki na kabilar Bade na nuna cewar, an somo shi run a wajen shekara ta 1820 to amma kuma wasu na cewar, a’ a an fara shi a shekara ta 1965. Kuma tun shekara ta 1994 rabo da sake gudanar da shi duk da cewar an gudanar da kwarya-kwaryar bikin a shekara 2014, tun lokacin rabe da sake yin wannan biki sai a wannan sheakara ta 2020 gwamnn Mai Mala Buni ya Samar da zunzurutun  kudi har Naira Miliyan 80 don kammaluwar bikin da suka hada da gyara hanyar shiga yankin da gyara wurin yin hidimar da sauran muhimman ayyuka.

Da yake jawabin yayin bude bikin, Gwamna Mai Mala  Buni, ya bayyana cewa gwamnatin sa ta yanke shawarar sake farfado da bikin raya al’adun gargajiyar tare da kamun kifin ne don yadda bikin yake cike da alfanun habaka hadinn kai, nishadantarwa kana da bunkasa tattalin arziki musamman ta wajen samar da kudaden shiga ga jihar da masarautar Bade da kuma karamar hukumar da ake gudanar da shi a ciki watau karamar hukumar Jakusko.

Gwamna Buni ya ce, “ko tantama babu kan cewa babu wata hanyar da za mu bunkasa tattalin arzikin mu ta fuskacin kiwon kifi ba tare da farfado da bikin kamun kifin da muke da shi a Bade ba, hadi da bikin raya al’adun gargajiya kuma dole mu dauki matakin gina su saboda nan gaba wato ‘yan baya.

Gwamnan ya bada umarni ga kwamishinan kula da harkokin kasuwanci da yawon bude-ido, da sauran hukumomi masu alaka da lamarin kan cewa, su dauki mataki wajen gyara kayan da suka kunshi harkokin raya al’adun gargajiyar tare da bikin kamun kifin, ba tare da jinkiri ba, a matsayin shirye-shiryen bukukuwan gaba in Allah ya so.

Ya kuma  sake bayyana cewa gwamnatin sa tana kokari wajen sake farfado da harkokin noma, kana ya shaidar da cewa gwamnatin sa za ta naxa kwamitin aiwatar da rahoton da kwararrun masa a fannin gona suka gabatar masa kan daukar ingantattun hanyoyin sake habaka aikin noma a jihar Yobe kasancewar al’ummar Yobe aksarinsu manoma ne na rani da damina da kuma kamun kifi.

Gwamnan ya kara da cewa, “Saboda haka babban kokarin da muke son aiwatar wa shi ne kafa kwamitin da zai lalabo mana sahihan hanyoyin da zasu kai mu ga tudun dafawa dangane da farfado da aikin noma tare da taka muhimmin matakin da zamu kasance a sahun gaba’ don Samar da madafa”.

A nasa jawabin shugaban majalisar dattawa kuma haifaffen wannan masarauta ta Bade Sanata Ahmed Lawan ya sha alwashin yin aiki tare da ‘yan majalisar dattijai wajen kokarin bunkasa bikin kamun kifi na Mauyi-Ganga, domin cin gajiyar jihar Yobe hadi da gwamnatin tarayya ta yadda nan gaba wannan biki zai zama Na kasa da NASA inda yin hakan zai sa ‘yan yawon shakawa su rika ziyarta wannan biki daga kowane bangare na duniya.

Ya kara da cewa “zai yi kokarin ganin ya gayyato wassu hukumomi tare da ma’aikatu daban-daban wajen aikin sake yashe kogin, wanda zai kara fadada shi. Wanda na riga mun fara tattauna batun tare da su don fara tsoma hannun su a gudanar da bikin raya al’adn gargajiya tare da kamun kifin ganin cewar, lamarin ba Na Jihar Yobe ba ne kadai, lamari da ya hada kasa baki daya.

A karshen gasar dai Sarakunan ruwa Na Gashuwa da na Gogaram sune suka zo na daya da na biyu wajen kamun kifi mafiya girma yadda gwamnatin Yobe ta basu mabambanta kyaututtuka KEKE NAPEEP ga na daya da kudade sai na biyu kyautar kudi kudan Naira dubu 300 jimlatan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here