Gwamna El- Rufa’i Cikakken Mai Kishin Talakawa Ne – Dakta Shinkafi

0
426
Mustapha Imrana Abdullahi
WANI mai rajin kare hakkin bil’adama da ke garin Kaduna Dakta Suleiman Aliyu Shinkafi ya bayyana Gwamna Malam Nasiru Ahmad El-Rufa’i, a matsayin Gwarzo cikakken dan kishin kasa mai kaunar ci gaban Talakawa a kodayaushe.
Dakta Suleiman Aliyu Shinkafi ya bayyana hakan ne a garin Kaduna inda ya ce “Wallahi Gwamna Malam Nasiru Ahmad El-Rufa’i duk ya fi sauran Gwamnonin baki daya saboda idan ya tsaya a kan batun gaskiya ba wata sauran magana”.
Ya ci gaba da cewa ka duba irin ayyukan da mutumin nan yake yi su ake cewa ci gaban al’umma.
“Na bi ta wajen Ofishin KASTELEA aikin hanyar da aka yi hakika an yi mai kyau kamar ba a kaduna mutum yake ba idan ya bi ta wurin”.
Ya kara da cewa da zarar ya samu ya kammala ayyukan da ya tasa a gaba shi kenan ya bude wa dukkan jama’a idanu nan gaba kowa zai zama Gwamna a Kaduna sai ya tashi tsaye sosai ya aiwatar da ayyukan ci gaban jama’a.Saboda haka ni da an ce in kawo mutum mai kishin al’umma Malam Nasiru Ahmad El-Rufa’i Gwamnan kaduna kawai zan nuna ba sauran wata magana.
Dakta shinkafi ya ce ga ayyukan manya manyan tituna ana ta yi a ko’ina duk domin jama’a wannan shi ne aikin mutane.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here