Hukumar Soja A Borno Ta Saki Wasu Tubabbun Mayakan Boko Haram Kimanin 1,400

0
827

Muhammad Sani Gazas Chinade, Daga Damaturu

GANIN cewar wassu da yawa daga cikin ”yan kungiyar Boko Haram na ajiye makamansu tare da mika kansu ga jami’an tsaro na tsawon lokacin don tuba da abin da suka yi a wannan karon ma gwamnatin jihar Borno ta bayyana cewa akwai kimanin tubabbun mayakan Boko Haram 1,400 da rundunar sojoji suka sako domin ci gaba da rayuwa a cikin al’umma, wadanda a baya ake tsare dasu bisa zargi da hannu a ayyukan tayar da zaune tsaye a tsakanin al’umma.

Bayanin hakan dai  ya fito ne daga bakin kwamishinan yada labarai a jihar Borno, Babakura Jato, a zantawar sa da manema labarai a garin Maiduguri.

Kwamishinan yada labari ya yi nuni da cewa, kimanin mayakan Boko Haram 1, 400 rundunar sojojin ta saka kusan a yanzu karo na uku a jere, tun bayan fara aiwatar da shirin ‘Operation Safe Corridor’ da aka kaddamar a baya.

Har walau an fara aiwatar da wannan tsarin ne a cikin shekarar 2016 wanda kuma aka dakatar har sai a 2018 yayin da sakin tubabbun ya fara gudana ka’in da na’in.

Babakura Jato ya kara da cewa, mafiya yawan wadanda ake sakin ba lalle ne su kasance mayakan Boko Haram din bane kai tsaye, face suna da alaka da ayyukan tada zaune tsaye ko kuma an kama su bisa kuskure a wani waje ko a wani lokaci mai sarkakiya.

Ya nanata cewa, “Sannan kuma ana sakin su ne lokaci bayan lokaci wanda ya gudana sau uku. Kason farko an sako su ne a lokacin tsohon gwamna Shettima, inda a lokacin Gwamna Zulum aka saki tubabbun aji biyu”.

“A cewarsa a jimlace, an saki tubabbun kimanin mutum 1,400. Kuma daga cikin wannan adadi na 1,400, mafiya yawan su wadanda ake zargi ne aka saki bayan an tantance su. Kuma mutane ne wadanda ake zargin su da kasancewa Boko Haram ba wai an tabbatar su din ba ne, ‘a’a; ana zargin su ne”.

“Ya kara da cewa sauran ne za ka tarar ‘ya’yan mayakan Boko Haram ne ko kuma hakikanin Boko Haram din ne. Sannan kuma a yanzu ba zan iya baka jedawali da adadin kowane sashe ba, saboda dalilan tsaro.”

kwamishinan yada labaran ya ce, jin irin korafe-korafen da ake yi nan da can ta wajen  zargin cewa wai wasu daga cikin tubabbun mayakan da ake sakin suna koma wa ga ayyukan su na ta’addanci, ka hakan a cewarsa yana da ja kan hakan, saboda mafi yawan wadannan zarge-zargen da ake yi basu da wani tushe.

A cewarsa ana sako tubabbun ne bayan sun samu horo kana da mika su a hannun gwamnatin jihar Borno, wanda ita kuma sai ta tsara sake mayar dasu zuwa cikin jama’a don su ci gaba da rayuwar su kamar a da.

Ya kara da cewa, ”kuma da zaran jama’ar garin irin wadannan mutanen sun ki amincewa dashi, saboda kasancewar sa dan Boko Haram a baya, shi ne sai gwamnati ta sauya wa mutumin wani gari don samun nutsuwa gudin kar ya sake komawa ga ayyukansa na baya abin ki.

Da manema labarai ke tambayrsa shi kan ko akwai wani korafi dangane da canjin shekar wassu daga cikin tubabbun zuwa ayyukan su na da, sai ya kada baki ya ce, “haka bai taba shigowa kunnuwansa ba, to amma kuma Muna samun labarin irin kalubalen da wadannan mutane me cin karo da shi a cikin al’ummominsu na kin sakin jiki da su daga al’ummominsu inda suke dawowa ga cibiyoyinsu don canza musu gari dabam.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here