Talakawa Ba Sa Amfana Da Wutar Lantarki Kamar Manyan Kasar – Mele Kyari

0
414

Daga Usman Nasidi.

BABBAN manajan daraktan matatar man fetur ta Najeriya, Mele Kyari ya nuna damuwar shi ta yadda rashin wutar lantarki ta yi katutu a kasar nan.

A yayin jawabi a taron tattalin azrki na man fetur din Najeriya wanda hakan har ta kai ga sun saka hannun kan wasu makuden kudi da USTDA ta ba da don aikin wutar lantarki a Abuja a ranar Talata, shugaban ya jajanta yadda ‘yan Najeriya ke fafutukar samun abin sakawa a bakin salati sannan kuma suke neman wutar lantarki. Ya ce wutar lantarkin ta zamo ta masu hannu da shuni.

Kyari ya ce kalubalen rashin wuta a Najeriya dole ne a shawo kanshi a gaggauce, kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Ya ce: “Ga wannan kasar da ma wasu da ke Hamada a Afirka, abin da kullum muke tunani shine abinci. Akwai mutane da yawa da basu iya cin abinci ko sau daya. Hakazalika kuwa wutar lantarki ta zama abin jin dadi kuma masu kudi ke samu.

“Mafarkin kowa ne ya mallaki janareto ko dan karami ne. Dole ne mu samo hanyar shawo kan rashin wutar lantarki da gaggawa. Mun san muna da iskar gas mai yawa kuma dole ne mu kirkiri ababen more rayuwa ta hanyar amfani da gas din.
“Dole ne su samu lantarki don samar da ayyukan yi da arziki mai yawa. Ta haka ne za mu samu zaman lafiya a kasar nan.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here