Niyyarmu Al’umma Su Gano Kurakurensu Su Gyara – T.Y Sha’aban

0
620
Musa Muhammad Kutama Daga Kalaba
SHARHIN sabon fim din Manta Sabo na kamfanin T.Y. Shaban kannywood  da ke Kano fim din kamar yadda wanda ya shirya shi ya bayar da umarni T.Y.Shaban yace fim ne da ke koyar da yadda mutum zai san yadda zai rika kare mutuncinsa da ma sanin hakkin kansa da ya rataya wuyansa da ma sauran jama’a . Kana mutum ya koyi darasi ashe ian mutum ya aikata haka laifi ne domin ya kiyaye kada ya aikata nune ga jama’a domin su kiyaye aikata wasu laifuka domin a samu zaman lafiya tsakanin jama’a.
GTK:Gabatar mana da kanka ?
T.Y.Shaban: Assalama Alaikum  Da farko dai ni  sunana T.Y.Shaban ni jami’i ne  mai shirya fina-finan Hausa ne ,kuma mai shirye-shirye a gidan Talabijin.
GTK:Fim din ka mai suna Manta Sabo menene makasudun shirya shi?
T.Y.Shaban :Mun shirya shi ne domin wayar da kan al’umma dangane da sanin dokoki na Final Kot saboda da dokoki na final kot suka zo ake amfani da su musamman a nan jihohin Arewa cin kasar nan musamman akwai laifuffuka da dama da al’umma suke aikatawa ba tare da sanin cewa abin da suka aikata laifi ba ne shi ne muke kokari mu dauko laifi daya daga cikin laifukan da ake aikatawa muka mayar dashi fim domin mu nuna yadda ake aiwatar da laifin za’a gani ta hanyar Dirama.
GTK:Nasan fim xin Manta Sabo na daya daga cikin fina-finai da suka fito a wannan sabuwar shekara ?
T.Y.Shaban: Haqiqa yana daya daga cikin su da aka saki jama’a sukakalla cikin wannan shekara ta 2020.
GTK:Ka yi fice a fagen shirya fina-finan Hausa da kuma gabatar da shirye-shirye a tashar Talabijin mai ya jawo hankalinka ka shirya wannan fim ?
T.Y.Shaban: A gaskiya duba da kwarewa da na yi da kuma sanin makamar aiki da na yi musamman wadanda suke zuwa qasashen waje ana nuna mana cewa mu riqa yin abubuwa da za su rika kasancewa akwai Ilmantarwa ,akwai  Nishadantarwa da  Fadakarwa,wurin al’umomi ko ba don komai ba koda bayan babu kai ya zamana wannan abun ya yi tasiri a rayuwa kuma ya zamana wani abune kayi shi sadaka mai gudana.
GTK: Jaruman da ke cikin fim din an yi amfani da sabbin fuskoki ne ko angauraya da tsofaffin hannu ganin cew aana samun sabbin jarumai dake tasowa?
T.Y.Shaban:To ya hada jarumai da yawa musamman akwai ni T.Y.Shaban akwai Mahmud Daneji,akwai Samira Ahmad akwai ‘yan wasa da dama dai a cikin fim da suka bayar da gagarumar gudunmuwar su .
GTK:Wane darasi fim ya koyaw aduk wanda ya kalleshi ga waxanda basu kallaba fa ?
T.Y.Shaban:In sha Allah fatan mu ga wadanda suka kalla da kuma za su kalla shine ya karu da sanin dokoki na final kot ya gane cewa fa abu kaza aikata shi  laifi ne kuma hukuncinsa kaza ne,idan ya aikata kaza kaza za’a yi masa .To wannan shi zai sanya al’umma su guje wa aikata laifi, sai a samu ingantacciyar al’umma, da zaman lafiya da kwanciyar
hankali .
GTK:Sakon ka ga masu kallon fina-finan T.Y.Shaban?
T.Y.Shaban: E! to sakona shi ne wadanda suke bibiyar mu ya kasance idan mun yi wani kuskure ko sunga wani kuskure da muka aikata a fina-finan mu a riqa sanar damu kuma yana da kyau a riqa bibiyar tasho shin mu Youtube da muke da su da fina-finanmu da suke zuwa gidajen Talabijin domin karbar gyara ma ya sa muke bayar da lamb ar wayoyin mu an hannu.A rika gaya mana inda muka sa domin mu rika gyarawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here