TUN GOWON NA SHUGABAN KASA NAKE YANKAR FARCE – DOKIYAL

  0
  573
  Musa Muhammad Kutama Daga Kalaba
  MUHAMMADU Mamman Dokayal  dattijo ne dan shekara 70 da haihuwa a duniya yake yawon sana’ar yankan farce ya zauna garurukan Anaca jihar Anambra da kuma Bayelsa ya ce ba zai taba mancewa da kudin da a tasa.Yace bana shekarar sa 44 yana gudanar da
  wannan sana’a shin ko zai ya  samu ba a Anaca  wata shekara ya je gida Dokayal da su karamar hukumar Toro jihar Bauchi har Naira dubu 4 da 500 kudi masu yawa da ya  taba samu a rayuwar. Wakilin mu na kudanci  a kalaba jihar kuros riba musa kutama ya yi
  kacibis da Dattijon a layin Bagobiri unguwar Hausawa yana gudanar da sana’ar ga yadda tattaunawar su ta kasance:-
  GTK:Baba gabatar mana da kanka?
  Muhammadu Mamman:Sunana Muhammadu Mamman Dokayal  karamar hukumar Toro
  jihar Bauchi.
  • MUH DOKIYAL BISA AIKINSA
  GTK: Mai ya kawo ka kalaba ?
  Muhammadu Mamman: Yankan Farce .
  GTK:Tun yaushe ka fara wannan sana’a ta yankan Farce?
  Muhamamdu Mamman:Tun lokacin Yakubu Gowon yana shugaban kasa,anyi yaki ke nan na basasa an gama na bulla Anaca muka je Anaca gidan sarkin Hausawan Anaca muka zauna anan muka yi aiki muka dawo Lokacin Murtala Ramat Muhammed yayi Mulki naci gaba da yankan farce har zuwa wannan lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari karo na biyu bayan mulkin soja da ya yi yake na farar hula yanzu ina yin wannan sana’a ta yankan
  farce. Tun daga lokacin da wadancan shugabanni suka yi mulki zuwa na yanzu tun daga Gowon zuwa Buhari nake yin wannan sana’a ban daina ba.
  GTK: Mai ya jawo hankalin ka kake yin sana’ar yankan Farce?
  Muhammad Mamman:E abinda ya jawo hankali na nake wannan sana’a a nan Kalaba na zo neman kudi ne kuma yau talata nake son komawa gida wurin iyalina can Bauchi, da na zo neman kudi na duba naga yankan farce ya fi ye mini to shi ne sai na kama.
  GTK:A wace shekara ka fara sana’ar yankan farce?
  Muhammadu Mamman: A shekarar da nayi Aure na haifi dana  Dahiru dagam nan na fara.
  GTK :kamar shekara nawa ke nan  yanzu?
  Muhammadu  Mamman: kamar shekara 44 .
  GTK:Tsawon wannan shekaru da ka fara yankan farce ko kwalliya ta biyakudin sabulu?
  Mahammdu Mamman:Tabiya ! Tabiya! Kwalliya ta biya kudin sabulu don har yanzu niacin abin da na samu a Anaca ma har yanzu yana nan har yanzu da sauran sa .
  GTK:Da yake ka shafe shekara 44 kana sana’ar yankan Farce ko ka taba yi wa daya ko  wasu daga cikin tsofaffin shugabannin kasar nan komanyan ‘yan siyasa ko masu mulki yankan farce?
  Muhammadu Mamman:A’a ban taba yi wa kowa yankan farce ba a cikin shugabannin nan ba.Amma akwai uwargidana ita tana siyasa ita ce ma shugabar mata jam’iyyar PDP  na Toro.
  GTK:Da kace kwalliya ta biya kudin sabulu wani zaiyi tunanin tunda shekaru sun mika kamata ya yi ka hakura a koma gefe aci abinda aka tara kana da yunkurin haka?
  Muhammadu Mamman : Nakan ga dan yawon da nake yi ina dan kokarin nan saboda jikina ya dan washe tun da ina da lafiya ina kalau dina ba zan zauna a gida ba sai dai yanzu idan na koma gida zan hakura in kama Noma .
  GTK:kamar ka jingine sana’ar ka ci gaba data Nima da Kiwo?
  Muhammadu Mamman: E !
  GTK: Yanzu idan ka koma mai za kayi?
  Muhammadu Mamman:Idan na koma gida aini manomi ne ina noman Gero da Dawa da kuma Tumatiri, Waken Soya, Wake .
  GTK:Wato za ka ajiye yankan farce ka rungumi Noma ?
  Muhammadu Mamman: E zan rungumi Noma gadan-gadan.
  GTK: Zaka iya tuna ranar da kayi wani yankan farce ka samu alherin da ba za ka iya taba mancewa da ita ba.?
  Muhammadu Mamman:Wanda ba zan taba mantawa ba akwai shekarar da na yi yankan Farce a Anaca na dawo da kudi  na samu kudi Naira dubu 4 da 500 na sayi Akuya ,Akuyar nan ta yadu har na sayi Saniya tana can a ruga
  yanzu hakan nan .
  GTK:ka taba yin yankan farce da ya jaza maka matsala da ba za ka iya mancewa da shi ba?
  Muhammadu Mamman:A’a babu wanda ya taba jaza  mani ko ya sanya ni matsala a rayuta sam.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here