An Sanya Dokar Hana Fita Ta Kwana Uku A Bayelsa

0
511
Mustapha Imrana Abdullahi
JAMI’AN tsaron ‘yan sanda a Jihar Bayelsa karkashin jagorancin Uche Anozia ta bayyana cewa sun sa dokar hana fitar ne sakamakon irin yadda tashin tashina ta barke a babban birnin Jihar na Yenagoa jim kadan bayan Dauye Diri na PDP ya karbi takardar lashe zabe daga hukumar zabe ta INEC.
Tarzomar dai ta barke ne tun bayan da hukumar zabe ta mikawa dan PDP Daiye Diri takardar lashe zabe a matsayin Gwamnan Jihar Bayelsa, lamarin da bai yi wa yayan Jam’iyyar APC dadi ba
Tun bayan da kotun kolin Nijeriya da ta yanke hukuncin cewa an samu matsala a takardun dan takarar mataimakin Gwamnan Jihar Bayelsa karkashin APC wanda suka tsaya tare da mai takarar Gwamnan APC da hukumar zabe ta bayyana David Lyon ya lashe zaben Gwamnan a kwanan baya da aka yi zaben Gwamna.
An dai sa dokar ne daga karfe 8 :00 na Yamma zuwa karfe 6:00 na safe na tsawon kwanaki uku daga yau Juma a zuwa ranar Lahadi mai zuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here