An Yi Garkuwa Da Babban Jami’in Gwamnatin Nasarawa

0
323

Daga Usman Nasidi.

WASU ‘yan bindiga sun yi garkuwa da sakataren dindindin na ma’aikatar ayyukan a jahar Nasarawa, Alhaji Jibrin Giza, a tsakar daren ranar Asabar.

Kwamishinan ‘yan sanda a jahar, Mista Bola Longe, ya tabbatar da lamarin ga manema labarai a Lafia.

Longe ya bayyana cewa yan bindiga sun sace sakataren din-din-din din daga gidansa a Shabu, wani yanki na Lafia da misalin 12:40 na tsakar dare zuwa wani wuri da ba a sani ba.

A cewar kwamishinan ‘yan sandan, Shugaban ‘yan sanda a yankin ya riga da ya zuba wasu jami’ai wadanda za su bi sahun masu garkuwan da suka tsere da wadanda suka sace.

Longe ya kara da cewa ya umurci mataimakin kwamishina na ayyuka, jami’in da ke kula da rundunar yaki da fashi na musamman, da su kakkabe yankin don tabbatar da sun ceto wadanda aka sace da kuma kama masu garkuwan.

Ya kuma sha alwashin cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba har sai ta ceto wadanda aka sace.

Longe ya kara da cewa masu garkuwan ba su kira yan’uwan wadanda suka sace ba tukuna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here