Ban Da Wata Niyyar Sake Aure A Yanzu – Inji Janar Babangida

0
347

Daga Usman Nasidi.

TSOHON shugaban kasar Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya musanta zargi da rade-radin da wasu jama’a ke yi inda ya bayyana cewa ba ya da niyar sake yin wani aure a halin yanzu.

Tsohon shugaban wanda marigayiyar tsohuwar matarsa Maryam ta kasance Uwargidar Najeriya na shekaru takwas tsakanin Agustan 1984 zuwa 1993. Ta rasu ta bar Maigidanta bayan sun shafe shekaru 40 tare.

Da take amsa tambayoyi daga kafafen yada labarai game da yadda yake rayuwar gwauranta a matsayinsa na ‘dan shekara 78 a duniya, Janar Babangida ya bayyana cewa ‘ya‘yansa suna taimaka masa.

Kwanakin baya an yi ta yadawa cewa Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya na neman Matar aure , amma wannan karo, ya ke cewa wannan aikin ‘Yan jarida ne kurum.

“Abin da ‘Yan jarida su ke so kenan. Mutane su na ta tambayata, na kuma fada masu cewa wannan abin da ku (‘yan jarida) ku ka fada ne, bai nufin abin da na fada kenan.”

Babangida ya na kallo Maryam Babangida ta mutu a gadon asibitin Amurka
“Ina da ‘Ya ‘ya masu fahimta da kula sosai; su na kokarin dasawa daga inda Mahaifiyarsu ta bari.”

Tsohon shugaban na Najeriya ya ce ‘Ya ‘yan cikinsa sun tisa daga inda Mahaifiyarsu ta bari. Maryam Babangida ta rasu ne a sakamakon fama da cutar daji watau kansa.

IBB ya tabbatar da cewa a wannan shekaru na sa, bai tunanin sake aure. A halin yanzu, tsohon Sojan ya ce babu abin da ya ke yi a yanzu sai dai hutu da barci da karatu.

Hakazalika da aka yi masa tambaya game da karatun Al-Kur’ani, Babangida, ya nuna cewa zai fi kyau a ce jama’a ba su san labarin yadda yake yawan karatun Al-Kur’ani ba.

Ibrahim Babangida ya auri Maryam ne daf da za a fara yakin basasa a shekarar 1969. Ainihin Maryam mutumiyar kasar Delta ce a yankin Kudu maso Kudancin Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here