Gwamnan Yobe Ya Amince Da Kebe Sama Da Naira Miliyan 220 Don Biyan Tsofaffin Ma’aikata

0
424
Muhammad Sani Gazas Chinade, Daga Damaturu

GWAMNA Mai Mala Buni na Jihar Yobe ya amince da kebe zunzurutun kudi har Naira miliyan 220, 759, 558.04 domin biyan tsuffin ma’aikata 180, wadanda suka yi ritaya daga kananan hukumomin jihar 17 a jihar.

Bayanin hakan ya zo ne a wata takarda ga manema labarai wadda ta fito daga ofishin kwamishinan yada labarai a jihar Yobe, Malam Abdullahi Bego a garin Damaturu.
Kwamishinan ya kara da cewa, a cikin adadin wadannan kudaden, za a kashe naira miliyan 163 da ‘yan kai wajen biyan tsoffin ma’aikatan da suka yi ritaya kuma suke nan a raye, yayin da sauran Naira miliyan 57 da ‘yan kai kuma, an ware su ne wajen biyan hakkokin ma’aikatan da Allah ya yi wa rasuwa, inda za a bayar da kudin ga iyalan su.
Bugu da kari kuma, Alhaji Bego ya kara da cewa, wannan adadin tsuffin ma’aikata aji na 39 da za su ci gajiyar kudaden su na sallama a kananan hukumomin, ya zo ne bayan aikin kwamitin tantance yan ritaya wadanda ke jiran hakkokin su na fansho da garatuti a kananan hukumomin jihar Yobe.
Har ila yau kuma, ko a cikin watan Disamban shekarar 2019 da ta gabata, Gwamna Buni ya bayar da umurnin ware akalla Naira miliyan 247 domin biyan tsoffin ma’aikata 194, a karo na 38, na jerin biyan tsoffin ma’aikatan kananan hukumomin jihar 17.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here