Kotu Ta Jefa Gwamnan CBN Na Bogi Gidan Kasu

0
349

Rahoton Z A Sada

WATA kotu a Najeriya ta yanke hukuncin daurin shekaru uku ga Nwalozie Onyebuchi Julius, wanda a kwanakin baya ake zarginsa da fakewa a matsayin Gwamnan Babban Bankin Najeriya wato Godwin Emefiele.

Mai shari’a Agatha Anulika Okeke ta Kotun Tarayya a garin Uyo reshen jihar Akwa Ibom ce ta yanke hukuncin, inda ta ce zai shafe shekaru uku a gidan yari ba tare da zabin biyan tara ba.

A kwanakin baya ne dai hukumar EFCC a Najeriya ta maka Mista Onyebuchi a gaban kotu kan zarginsa da yin sojan gona da sunan gwamnan CBN tare da yin damfara da ta kai ta naira miliyan 4.5.

A Disambar bara ne hukumar EFCC reshen jiyar Uyo ta samu bayanan sirri kan almundahana da ake yi a shafukan intanet a jihar, wanda hakan ya kai ga kama Mista Onyebuchi.

Jim kadan bayan Mista Onyebuchi ya shiga hannu, ya amince da aikata laifin da ya yi, haka zalika a wata kwamfutarsa kirar HP da aka yi bincike a kanta, an samu hujjoji da suka nuna ya aikata laifukan da suka hada da damfara da wasu laifuka da ake yi a intanet.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here