Isah Ahmed Daga Jos
KUNGIYAR matasa ta Kwankwasiya ta Jihar Filato, ta yi bikin yaye mata guda 600, da ta dauki nauyin koya masu sana’o’i daban-daban, a garin Jos a kashen makon da ya gabata.
An gudanar da taron bikin yaye matan ne, a daki taro na babban masallacin juma’a da ke garin Jos.
Da yake jawabi a wajen, tsohon gwamnan Jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yabawa kungiyar kan wannan kokari da tayi, na daukar nauyin koyawa matan sana’o’i.
Ya ce wannan aiki yana daya daga cikin tsare tsaren Kwankwasiya na taimaka wa al’umma.
‘’A tsarin kwankwasiya a jihar Kano, an dauki ‘ya’yan talakawa wadanda ba su san kowa ba, an biya masu kudaden karatu, sun tafi waje sun karanto fannoni da dama. Wannan shi ne muke bukata a taimaki mara shi ya tashi, shi ma ya taimaki wani’’.
Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso wanda Alhaji Bashir Sanata ya wakilta, ya yi bayanin cewa babu shakka idan ana taimaka wa matasa ana basu ayyukan yi, ana koya masu sana’o’i kamar yadda wannan kungiya tayi, za a magance matsalar tsaron kasar nan.
Ya ce da yawa aure yana mutuwa, saboda maigida ya fita bai bayar da kudin cefane ba.
Don haka idan aka tallafa wa mata aka koya masu sana’o’i suka dogara da kansu, za su rike gidajensu su bai wa yara tarbiya. Kuma wata rana ko maigida bai bayar da kudin cefane ba, mace za ta iya yin wani abu.
A nasa jawabin shugaban kungiyar matasan Kwankwasiya ta Jihar Filato Alhaji Sudais Salim ya bayyana cewa sun shirya taro ne, domin su yaye mata 600 da suka dauki nauyin koya masu sana’o’in, dinki da kwalliya da girke girke da man shafawa da man zafi da dai sauransu.
Ya ce sun tallafawa matan ne domin su sami abin dogaro da kan su, ganin cewa sune garkuwar al’umma gabaki daya, da kuma tausaya masu, ganin kuncin rayuwar da ake ciki a kasar nan.
Har’ila yau ya ce baya ga wannan, sun yi ayyukan kai ziyara gidajen yari da gidajen marayu da asibitoci da makarantu suka tallafa masu.
Ya ce nan bada dadewa zasu fara shirye shiryen auren zawarawa a Jihar Filato.
Ya ce saboda ganin ayyukan alherin da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso yake yi ne, ya sanya suka kafa wannan kungiya, don su yi koyi da shi.