Limamin Ci Gaba Da Canza Fasali Ne Gwamna El-Rufa’i –Inji Hukumar Zartaswar NNN

0
395

HUKUMAR zartaswar kamfanin buga jaridun Gaskiya Ta Fi Kwabo da New Nigerian Newspapers na kullu yaumin da ta ranar Asabar da ta Lahadi sun bayyana Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Amad El-Rufa’i a matsayin mutum daya tamkar da goma wajen kawo ci gaba da canza fasalin jihar ta hanyar dimbin ayyukan raya kasa, wanda hakan abin alfahari ne ga daukacin shugabannin hukumar zartaswar na NNN ga wannan mulki na Gwamnan.

Wannan batu ya fito ne a wata takardar da ta sami sanya hannun Editoci da mahukuntan kamfanin jaridun na NNN wadda aka rubuta wa Gwamna El-Rufa’i  don nuna jin dadi tare da taya shi murnar cika shekaru 60 a doron kasa wanda aka gudanar da shi a ranar Lahadin da ta gabata, wato 16 ga watan abrairu, 2020.

Wasikar da ta fito daga kamfanin na NNN don taya wannan gwarzo murna a ranar 17 ga Fabrairu, 2020 ta sami sanya hannun Mukaddashin Manajan Daraktan kamfanin, Alhaji Yusuf Musa inda wasikar na cewa, jihar Kaduna da ma Najeriya kwata na da abin kwaikwayo na hazikancin wannan limamin ci gaban al’umma da canza fasali.

Wasikar har ila yau ta ce, ‘’ ilahirin mambobin hukumar zartaswar da ma’aikatan kamfanin na NNN na mika jinjinarsu da godiyarsu ga MalamNasir El-Rufa’i  shugaba mai hangen nesa, mai sanya kyakkyawan zato ga kirazan al’umma, uba kuma limamin ci gaba a bisa bikin cikarsa da Allah ya nufa na shekaru 60 cur a duniya.

‘’Ya mai girma Gwamna, dimbin ayyukanka da suka shafi al’umma kai tsaye kadai sun kara daukaka darajarka a tsakanin ‘yan uwanka masu mulki a wannan kasa. A gaskiya muna alfahari da samun mulkinka’’.

Wasikar ta ci gaba da cewa, ‘’Tsayuwarka tsayin daka babu barci kan batun kamfanin na NNN kadai na nuni da cewa, ma’aikatan kamfanin suna da Uba mai kula da su, kuma za su ci gaba da yi masa wulaya kodayaushe’’.

Ma’aikatan NNN ko shakka babu suna ci gaba da yi masa fatar alheri da addu’o’i kamar yadda ya taimaka wa rayukan al’umma da damar gaske da kuma yadda yake ta kokarin dawo da martabar jihar ta Kaduna, suna rokon Allah ya ci gaba da yi masa jagora ya daukaka shi tare da sanya masa albarka a lafiyarsa, sanya masa basira da hikima da tsawon kwana don ya ci gaba da yi wa al’umma hidima don ceto rayukansu.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here