Shugaba Buhari Ya Yi Roko Bayan Kashe Mutum 30 A Katsina

0
373
RahotonZ A Sada Da Rabo Haladu
MASANA na ci gaba da tsokaci a kan kiran da shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa al’ummar kasar nan  da su daina yanke wa kawunansu hukunci game da hare-haren ‘yan fashin daji.
Kiran na zuwa ne bayan hare-haren ramuwar gayya da wasu ‘yan bindiga suka kai wa wasu kauyukan karamar hukumar Batsari a jihar Katsina cikin karshen makon jiya inda aka kashe akalla mutum 30.
Shugaba Buhari ya yi kiran ne a wata sanarwar jaje kan hare-haren, wadda kakakinsa Garba Shehu ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Ya ce kashe mutane don ramuwar gayya bai dace ba kuma babu wanda ke da ikon daukar doka a hannunsa.
Yinramuwargayya.
Amma mai sharhi kan lamurran tsaro Kabiru Adamu ya ce ba ya jin kiran shugaban zai yi wani tasiri sosai saboda yadda ‘yan Najeriya suke ganin jami’an tsaro suna gaza aiwatar da ayyukansu.
Ya ce “kira ne mai kyau kuma dama duk wani shugaba ya kamata ya yi irin wannan kiran amma matsalar ita ce dole ne ke sa mazauna kauyuka a Najeriya daukar matakin tsaro a hannunsu.”
A kauyuka da yawa idan aka kama masu laifi jami’an tsaro ba sa tabuka komai kan masu laifi, wani lokaci sai a sake su ba tare da an yi masu hukunci ba, wani lokacin ma idan aka kai hari wasu kauyukan babu jami’an tsaron kwata-kwata a cewar Kabiru Adamu.
“Harkar tsaro kusan ita ce wajibi ga dan Adam, kuma alkawarin da ke tsakanin hukuma da dan kasa shi ne samar da tsaro amma idan aka gaza dole ne dan kasa ya dauki mataki da kansa” in ji Kabiru Adamu.
Sai dai ya ce sauya tsarin yadda ake tafi da lamurran tsaro na iya kawo mafita.
“Gwamnatin tarayya ta yi katutu a harkar tsaro ita kadai kuma ga shi ba a samun biyan bukata.
“Idan ta shigar da jihohi da masarautu da kungiyoyi masu zaman kansu, sannan ta horar da hukumar ‘yan sanda kuma a tabbatar da an hukunta duk wani mai laifi, za a iya samun saukin matsalar,” a cewarsa.
A baya-bayan nan dai, wasu jihohin arewa maso yammacin na fuskantar karuwar hare-haren ‘yan bindiga inda ake rasa rayuka da gidaje da dabbobi.
Da yawa daga cikin hare-haren na ramuwar gayya ne tsakanin wasu al’ummomi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here