‘Yan Fashi Sun Kwace Jarirai, Sun Jefa Cikin Wuta A Gaban Iyayensu

0
362

Daga Usman Nasidi Da Z A Sada

SHUGABAN karamar hukumar Batsari da ke Jihar Katsina a ranar Litinin ya bayyana yadda harin da aka kai musu a makon da ya gabata ya haddasa kisan mutane da yawa a yankin.

Akalla Mutane 30 suka rasa rayukansu a cikin kauyen Tsawwa da Dankar.

An bayyana cewa daga cikin mutane 21 da aka kashe a garin Tsauwa, banka wa 13 wuta aka yi har lahira.

“Yan fashin sun kwace jarirai sun jefa wuta a gaban iyayen su,” Shugaban Kauyen,Ibrahim Zangina ya bayyana wa Gwamna Aminu Bello Masari yayinda ya kai ta’aziya ga wanda suka tsira.

Bisa ga bayaninshi, Yan fashin sun shiga kauyen haye kan Babura kimanin 180 duk dauke da akalla
mutum biyu zuwa uku sannan suka fara harbin duk wanda suka ci karo da shi.

Ya kara da cewa harin ya faru ne yayinda ake sallar la’asar inda yace “S un harbi mafi akasarin masu alwala.“

“Sun harbi dabbobi da dama sannan sun kona amfanin gona, bamu taba fuskantar harin yan fashi irin wannan ba. A cewar sa.

Har wa yau , Shugaban Kauyen Dankar, Muhammad Suhura, ya bayyanama Masari cewa wasu daga cikin jama’an kauyen sun tsira akan dabbobin su.
Masari yayi Allah wadai da lamarin sannan ya roki wadanda suka bar kauyen dasu dawo.

Gwamnan ya bayyana cewa basuyi garkuwa da kowa ba amma anyi asarar rayuka da amfanin gona.

Ya ce gwamnati zata dauki mataki kuma kuma ya tabbatar da cewa hakan bazai sake faruwa ba, kuma ya dauke shi a matsayin kaddara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here