Ba Zan Ce Komai Ba Tukun Kan Barazanar Shekau – Sheikh Pantami

0
552
Sheikh Dr Isa Aliyu Pantami, Ministan Ma'aikatar Kimiyya Da Fasaha

Daga Usman Nasidi.

MINISTAN sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dakta Isa Ali Pantami, a ranar Litinin ya ki yin tsokaci kan barazanar da shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya yi masa.

Yayinda manema labarai suka tare sa a makarantar sakandaren gwamnati da ke unguwar Garki, Abuja, inda ya gabatar da lakca kan ilmantar da matasa ta hanyar zamani, ministan ya ce “Babu abin da zan ce yanzu“ kan barazanar.

Za ku tuna cewa shugaban kungiyar ta’addanci na Boko Haram, Abubakar Shekau ya yi barazanar kashe babban malamin Ahlussunnah, kuma ministan sadarwa, Isa Ali Pantami da fitaccen mai fashin baki a kan kungiyar Boko Haram, Audu Bulama Bukarti.

Shekau ya bayyana haka ne cikin wani sabon bidiyo daya fitar mai tsawon mintuna 15 da dakika 20, inda ya yi amfani da damarsa ya caccaki Sheikh Isa AliPantami.

Shekau ya kalubalanci Pantami kan cewa ba shi da hurumin yin magana da yawun Musulunci, sa’annan ya bayyana shi a matsayin mutumin dake ma kafirai aiki, haka zalika ya soki lamirin Pantami na kirkiro dokar hana mallakar layukan waya da suka wuce uku.

Shekau ya tuna ma Pantami yadda suka kashe Sheikh Jaafar Adam, wanda aka bindigeshi a yayin da yake sallar Asubah a Masallacinsa dake Kano, sa’annan ya yi kira ga sauran yan ta’adda dake Afirka dasu shiga farautar Pantami a duk inda suka gan shi.

“ Ya yan uwana dake nahiyar Afirka, Najeriya da ma ko ina, abinda muka ma Jaafar ba wani abu bane, dole ne a yanzu mu dauki mataki a kan Pantami a duk inda muka gan shi.” Inji shi.
Bugu da kari Shekau ya gargadi shugaban kasa Muhammadu Buhari , babban hafsan sojan kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai, gidan rediyon BBC, rediyon DW, rediyon Faransa da Dandan Kura Radio.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here