El-Rufai Ya Gabatar Wa Da Alkalan Babbar Kotu Manyan Motocin Alfarma Guda 24

0
318

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

GWAMNA Nasir El-Rufai na jahar Kaduna ya gabatar da manyan motoci kirar Jeep guda 24 ga alkalan babbar kotu, duk daga cikin kokarinsa na inganta jin dadin jami’an bangaren shari’a a jahar.

Gwamnan, a yayin gabatar wa da alakalai motocin a Kaduna ya bayyana cewa za a samar da karin motoci ga sauran alkalai.

El-Rufai ya kuma bayyana tsare-tsaren gwamnati na gina wa alkalan gidaje.

“Wadanda za su amfana na gaba sune Khadis na kotun daukaka kara na shari’a da alkalan kotun daukaka kara na al’ada, In shaa Allah kwa nan nan za a gabatar masu da su, ba wai alkalai masu shigowa kadai ba a’a harma da wadanda suke nan tun da can.

“Gwamnatin jahar na shirin samar da gidaje ga manyan akalai, domin a yanzu alkalai na zaune ne a ginin gwamnati daban-daban a fadin jahar.

“Mun yar da cewa idan har muka samar da gidaje inda dukkanin manyan lauyoyi za su kasance cikin wadata, da wajen shaktawa da wajen siye-siye, za su kasance da wadatar zuci da ingantaccen tsaro.

“Muna aiki kan haka kuma kwanan nan masu aiki za su tunkari shugabannin kotuna don duba tsarin da zai fi dacewa,” in ji shi.

Gwamnan ya kara da cewa gwamnati na aiki kan tsarin gine-gine na bayan ritaya ga ma’aikatan shari’a, domin yana daya daga cikin lamuran da suka addabi mafi akasarin ma’aikatan gwamnati yayinda suke tunkarar yin ritaya.

Ya kara da cewa, gwamnati na shirin samar da cibiya guda ga dukkanin kotuna Kaduna maimakon yadda suke a tarwatse a wurare daban-daban.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here