Jajirtaccen Jan Gwarzo Ne Kai, Muna alfahari Da Hakan – Kamfanin Jaridar New Nigerian Da Gaskiya Ga El-Rufa’i

0
461

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

HUKUMAR zartarwa da Ma’aikatan kamfanin buga Jarida ta New Nigerian newspapers Limited da Jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo sun bayyana gwamna Malam Nasiru El-Rufa’i a matsayin jajirataccen jan gwarzo wanda ya kware wajen gudanar da aiyuka musamman wanda ya shafi inganta rayuwar al’umma.

Ma’aikatar ta bayyana hakan ne a cikin wata takardar da ke dauke da sa hannun mukaddashin shugaban kamfanin Yusuf  Musa Kwantagora, a wani sakon taya murna da suka aikawa gwamnan Malam Nasiru El-Rufai a bisa cikarsa shekaru sittin da haihuwa wanda bukin ya gudana a ranar litinin data gabata.

Shugaban Yusuf  Kwantagora, ya kara cewa gwamna Malam Nasiru El-Rufai shugaba ne wanda ya kasan mutumin mutane wanda yake aiki ba dare ba rana don ganin ya biyawa al’umma bukatunsu ba tare da ya nuna gazawa ba, kana da jajircewa wajen ganin ya kawo ingantaccen ci giba ciki da wajen fadin jahar gaba daya.

Takardar ta bayyana cewa El-Rufai shugaba ne na al’umma wanda akoyaushe al’ummarsa ne damuwarsa wanda hakan ya sanya yake iya bakin kokarinsa wajen ganin ya warware matsalar al’ummar wannan kamfanin ta New Nigerian da Gaskiya ke fuskanta ta hanyar ganin an biya su duka hakkokinsu cikin lokaci.

Ta ce “ tabbas muna alfahari da kai da gwamnatin ka da irin salon tsarin mulkin ka kana da yadda kake gudanar da aiyuka musamman wajen ganin ka inganta rayuwar al’umma da Jihar Kaduna ta duk hanyar da ta dace, wanda hakan ya sanya kayi zarra da fice ko a cikin tsaran ka ga baki daya ko a cikin kasar”

“ Mai girma gwamna, ayayin da kake ci gaba da kokarin ganin ka inganta rayuwar al’umma, kana da ganin ka dawowa da jihar Kaduna martabar ta, muna mai maka addu’ar fatan Allah Ya taimake ka, Ya saka maka da alheri, Ya baka yalwar lafiya, Ya yi maka albarka, Ya kara maka basira, Ya baka tsawon rayuwa wanda zaka ci gaba da anfanar rayuwa da al’umma baki daya.

A karshe, hukumar da ma’aikatan kamfanin sun godewa gwamnan Malam Nasiru El-Rufai bisa kokarin da yake a kansu don ya nuna shi Uba ne, mai ceton rayuwa, kana jigo wanda ke da zummar kawo ingantaccen canji ga rayuwar al’umma a kasa baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here