Ka Da Ku Ga Laifin Amaechi Idan Ya Tsere Wa ‘Yan Bindiga – Shehu Sani

0
350

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

TSOHON Sanatan Kaduna ta tsakiya kuma mai rajin kare hakkin bil Adama Sanata Shehu Sani ya yi martani game da rahotannin da suke ta yawo na cewa Ministan sufurin Najeriya, Rotimi Amaechi, ya sha da kyar a hannun ‘Yan bindiga.

Tsohon ‘Dan majalisar ya maida martani ne ga rade-radin cewa ‘Yan bindiga sun kai hari a tashar jirgin kasan da ke Garin Kaduna, inda aka ce har Ministan yana ciki.

Shehu Sani ya yi magana cikin ba’a, yana nuna cewa bai kamata a ga laifin Mai girma Ministan sufurin idan ya tsere wa ‘Yan bindiga domin ya ceci rayuwarsa ba.

Sani ya fito shafinsa na Tuwita a Ranar Litinin ya na cewa: “Gaskiya ne ko ma dai karya, ka da ku ga laifin Minista idan ya sheka a guje kamar wani Usain Bolt.

Sanatan ya kuma kara da cewa: “Wadannan ‘yan bindiga ba su san wata Majalisar zartarwa ta FEC ba. Toh, shin idan kai ne ba za ka gudu ba, wai don ka na Minista?”

Ministan sufurin kasar ya karyata cewa ya an kai masa hari, a cewarsa ya na barci salin-alin a Kaduna aka rika kiransa a wayar tarho bayan rade-radin ya shiga ko ina.

A baya Sani ya taba bada labarin yadda ya ga wani babban Soja a jirgin kasa duk da a lokacin Sojoji su na ikirarin sun lallasa Miyagun da ke kan titin Abuja zuwa Kaduna.

Sani ya wakilici Kaduna ta tsakiya ne a majalisar dattawan Najeriya a majalisa ta takwas, kuma ya kan fito ya yi magana a shafukansa na Tuwita da Facebook bini-bini.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here