An Tallafa Wa Mutanen Bakali

0
443
Rahoton Mustapha Imrana
SHUGABAN karamar hukumar Giwa Alhaji Abubakar Shehu Lawal Giwa ya tallafa wa mutanen garin Bakali da ke gundumar masarautar Fatika cikin karamar hukumar Giwa a Jihar Kaduna.
Shugaban ya kai masu kayan da suka hada da Buhunan Masara 30, Buhunan Shinkafa 20, Katifu 30, man Gyada jarkan 25, sai Zannuwa 50 da kuma Shadda 50, an dai kai masu wadannan kayan tallafin ne domin su samu saukin matsalar yan ta’addan da suka kai masu hari a cikin satin da ya gabata.
Abubakar Shehu Lawal Giwa ya kuma yi masu alkawarin ganin hakan ba ta sake faruwa ba saboda kamar yadda ya bayyana cewa yana ta kokari ba dare ba rana domin ganin ya sadu da wadansu cibiyoyin bayar da agaji ta yadda za a ci gaba da tallafa wa mutanen garin Bakali da ke karamar hukumarsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here