Isah Ahmed Daga Jos
‘YAN kungiyar fansho ta Najeriya, reshen Karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna, sun bukaci uwar kungiyar ta Jihar Kaduna, ta shirya masu zabe don sake zaben shugabannin kungiyar. Ganin wa’adin shugabannin kungiyar ya kare, tun a shekarar da ta gabata. ‘
Da suke zantawa da wakilinmu a madadin ‘yan fanshon, Mista J. B. Ladan da Mista Tambaya Yango da Malam Muhammed Rabi’u Abubakar sun bayyana cewa, babbar damuwar da take damun ‘yan fanshon Karamar Hukumar Lere. Ita ce shugabannin kungiyar, wa’adinsu ya cika amma sun yi ta zarce, batare da yin zabe ba.
Suka ce ya kamata yadda ake yin zabe a wurare daban daban a wannan kungiya, nan ma ayi zaben don a zabi shugabannin kungiyar.
Suka ce amma a lokacin da ya kamata ayi zaben, suna zaune sai muka ji cewa wai, an bar shugabannin nasu da wa’adinsu ya cika, su zarce batare da yin zabe ba.
‘’Maganar zarcewar shugabannin ya kamata ya zamanto da amincewar ‘yan kungiyar ne, ba daga wani waje ba. Kuma a cikin jerin shugabannin da aka ce su zarce, akwai wadanda basa ciki, amma aka sanya sunayensu aka ce su zarce tare da shugabannin. Gaskiya babu adalci a wannan waje. Don haka muna son ayi mana adalci a shirya mana zaben shugabannin wannan kungiya. Tun da wadanda suke kai, wa’adinsu ya cika tun a shekarar da ta gabata’’.
‘Yan fanshon sun yi bayanin cewa sun wakilta wasu sun tafi Kaduna, don jiyo gaskiyar maganar cewa an an baiwa wadannan shugabanni dama su zarce. Amma sai suka karyata wannan magana. Kuma uwar kungiyar ta kafa kwamiti yazo Saminaka yaji abubuwan da suke faruwa, amma har yau basu ji komai ba daga uwar kungiyar.
Suka ce tun a wata 11 na shekarar da ta gabata, wa’adin wadannan shugabanni ya kare. Don haka sun yi kira ga shugabannin kungiyar na Jihar Kaduna, su yi masu adalci ta hanyar shirya masu zaben sababbin shugabannin kungiyar. Musamman ganin yanzu ana zamanin mulkin damakoradiya ne.
Wakilinmu ya tuntubi shugaban kungiyar ‘yan fanshon na Jihar Kaduna, Alhaji Abdu Kwarbai don jin ta bakinsa kan wannan al’amari. Ya sheda wa wakilinmu cewa ya riga ya kafa kwamiti, kan wannan al’amari kuma yana jiran rahotan kwamitin ne.