Sun Roki Gwamna Ganduje Ya Biya Su Kudaden Sallama.

0
390
Daga Jabiru A Hassan, Kano.
MA’AIKATAN da suka bar aiki a jihar Kano sun nemi Gwamnan jihar Dokta Abdullahi Umar Ganduje da ya biya su hakkokin su na sallamar aiki musamman ganin yadda aka dauki dogon lokaci ba’a sami damar biyan wadannan kudade na sallama ba.
Cikin wadanda suka tattauna da wakilinmu sun nunar da cewa yana da kyau Gwamna Ganduje ya biya kudaden barin aiki domin mutane suna cikin wani hali na bukatar taimako saboda yadda rayuwa take a wannan  zamani, , sannan a cewar su, mafiya yawan wadanda suka bar aiki suna da nauye-nauye a kansu na harkokin iyali da zamantakewa.
Haka kuma sun sanar da cewa suna sane da halin da ake ciki na kokarin biyan su kudaden sallamar aiki, don haka za su ci gaba da addu’a ga Gwamna Ganduje domin samun ikon sauke wannan nauyi nasu tareda jaddada  yin  biyayya ga manufofin gwamnatin domin ganin ta cimma nasara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here