Jabiru A Hassan, Daga Kano.
A kwanakin baya ne, shugaban hukumar sauraren korafe-korafen al’uma wato “Securities and exchange commission” Alhaji Danladi Mohammed ya kai ziyarar kulla dangantakar aiki tsakanin hukumomin biyu cikin makon da ya gabata, inda ya bayyana cewa zasu yi aiki tare domin ganin al’amura suna tafiya cikin nasara kuma kamar yadda ake bukata.
Sannan ya jaddada cewa hukumar sa tana bukatar taimakon hukumar sauraron korafe-korafen al’uma domin tabbatar da cewa ana samun masalaha tsakanin bangarorin da suka sami rashin fahimtar juna dangane da wasu abubuwa da suka shafi hakkoki ta fannoni daban-daban na zamantakewar al’uma.
Alhaji Danladi ya kuma yi amfani da wannan dama wajen sanar da al’uma cewa hukumar su itace take kula da zuba jari da kyautata hadahadar kudade ta yadda kasuwannin hannayen jari zata zamo abar amincewa ga al’uma musamman ganin yadda ake samun sauye-sauye ta fuskar kaauwancin hannayen jari a duniya baki daya, sannan ya yabawa hukumar sauraron korafe-korafen al’uma saboda kokarin da suke yi na sasanta dukkanin wata matsala cikin masalaha kamar yadda ake gani a kullum.
Da yake maida jawabi, kwamishinan hukumar sauraron korafe-korafen al’uma na jihar kano Alhaji Ahmad Ado Dadinkowa yayi alwashin yin aiki da hukumar kula da hannayen jari domin samar da kariya mai gamsarwa ga dukkanin masu hadahadar hannayen jari tareda hada karfi da sauran takwarorin ta dake shiyyar kano domin tabbatar da cewa ana gudanar da harkoki cikin aminci da amincewa.
Dukkanin shugabannin suna tare da manyan jami’an su wanda hakan ta sanya ziyarar zata ci gaba da bude hanyoyin hulda tare wajen yin aiyukan kyautata kariya ga masu zuba hannayen jari wadanda hukumar ke kula dasu tun da aka kafata kuma ta fara aiki cikin shekara ta 1980.