An Kama Matar Da Take Auren Maza Biyu

0
491

 

Rabo Haladu Daga Kaduna

Matar mai suna Hauwa kulu mazauniyar unguwar Mariri tana zaune da mijinta na farko mai suna Bello sai rashin lafiya ta same shi ita kuma ta saka shi a mota ta aike da shi garinsu.

Daga bisani kuma ta dawo ta ci gaba da zamanta, shi kuma yana can yana jinya sai mijin da ta aura na biyu ya gamu da ita ta kuma shaida masa ita bazawara ce, inda nan take ya zare kudinsa har Naira dubu Ashirin ya biya sadaki.

Da yake direba ne ya hau motarsa ya tafi nema, daga bisani ta kira shi ta ce da shi an daura musu aure lokacin da ya dawo gidansa dakin amarya suna soyewa, sai mijin Farko ya bayyana ko da zuwansa sai ya gamu da wani mutum a cikin dakinsa nan da nan ya kwarma ihu, shi kuma mijin na biyu ya ce yana tuhumarsa da shigar masa gida ba tare da izini ba.

Nan da nan rikici ya kaure har zuwa ofishin hukumar Hisba da ke yankin ƙaramar hukumar Kumbotso.

A nata bangare wannan mata mai auren maza biyu ta bayyana cewa ai mijin farko wato Bello ya sawwakemata inda shi kuma yace wannan magana ba dashi aka yi taba.

Malam Bala shi ne mijinta na biyu yace shifa matarsace kuma babu Wanda zai rabashi da ita Tunda yanzu ma harta haifa masa yaro guda duk da yake a can baya suna da yara shida da tsohon mijin nata.


LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here