Gwamnatocin Binuwai Da Taraba Sun Dauki Matakan Kawo Karshen Rikici A Tsakaninsu

0
291
Rabo Haladu Daga Kaduna

JAMI’AN hukumar kula da kan iyakoki na Najeriya wato Nigeria Boundary Commission zasu fara shata iyakoki nan ba da jimawa ba.

Hukumar shata iyakokin Najeriya ta jagoranci wani gangami a Jihar Benue da Taraba da nufin fadakar da mutane akan shirin da ta ke yi na fara shata iyaka tsakanin al’ummomin biyu.

Mataimakin gwamnan Jihar Binuwai Engr. Benson Abonu da takwaransa na Taraba Haruna Manu, shugabanin al’umman jukun da kuma na Tibi sun sha alwashin kawo karshen tashe-tashen hankulan dake faruwa kan iyaka a tsakanin al’ummomin jihohin biyu.

Dafatan cewa, wannan aiki da za a gudanar, zai taimaka wajen samun fahimta tsakanin al’ummomin biyu ya kuma samar da zaman lafiya tsakaninsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here