Komawa Ga Allah Ne Babban Maganin Cutar Korona-Sheikh Sulaiman

  0
  938
  Sheikh Muhammad Sulaiman Abu Sulaiman

  Isah  Ahmed Daga Jos

  SHEIKH Muhammad Sulaiman Abu Sulaiman shi ne  babban Limamin Masallacin Sultan Bello, da ke Kaduna.  Kuma malami ne  a sashin tsangayar koyar da ilmin addinin musulunci, ta jami’ar Jihar Kaduna.

  A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu, kan cutar numfashi ta Korona da ta yadu a duniya, ya bayyana cewa komawa ga Allah ne babban maganin wannan cuta. Ga yadda tattaunawar ta kasance:-

  GTK: Mene ne za ka ce dangane da annobar cutar Kurona  da yanzu ake fama da ita a duniya?

  Sheikh Sulaiman: Wadannan cututtuka da suke faruwa annoba ce. kuma Allah madaukakin sarki yana aiko da annoba  ne, ga al’ummar da ta fandarewa dokokinsa. A kowace kasa idan aka sami al’umma, da barnarta ya yi yawa, sai Allah ya jefa masu wata annoba.

  Saboda Allah madaukakin sarki yana cewa runduna ta sojojin ubangijinka, babu wanda ya san adadinsu, sai shi. Don  haka sai muga wata kasar rundunar da za a tura masu, shi ne girgizar kasa, wata kasar ambaliyar ruwa, wata kasar gobara, wata kasar  kuma a tura masu cutar amai da gudawa.

  Nana A’isha ta tambayi Manzon Allah SAW mene ne cutar annoba? Sai ya ce cutar annoba wata cuta ce da Allah madaukakin sarki yake azabtar da bayinsa da ita, idan barna ta yi yawa.

  To kaga  yanzu duniya ta rikice, ko’ina barna ake yi,   an mayar da giya ta zama kunun zaqi. Zina da luwadi sun zama ko’ina ana yi,  wato maza su nemi maza, mata su nemi mata har dabbobi mutane suna nema yanzu.

  Kuma idan ka koma  bangaren cin amana da sata da zubar da jini, duk wadannan abubuwa suna jawo annoba. Idan ka koma ga mu’amula, a kowanne bangare ana cutar juna. Ma’aikatan gwamnati suna cuta, ‘yan kasuwa  suna algus, manoma da ‘yan makaranta da malaman makaranta, duk suna cuta. Wato idan ka dubi duniyar gabaki daya, kamar yadda Allah madaukakin sarki ne yake bayyanawa, cewa barna ta faru da yawa, a cikin kasa da ruwa da sararin samaniya. Babu inda za ka je face sai ka sami barna.

  Saboda haka Allah yake aiko da annoba ko mutane za su gyaru, su dawo ga dokokin Allah.

  Idan annoba irin wannan ta faru, bata ware wata kasa a duniya. A ce wannan kasar don ba kasar musulmai ba ce, babu ruwanta ko kuma don wannan kasar musulmi ce babu ruwanta.

  Idan ka lura akwai annobar da Allah ya jefa wa kasashen musulmi. Ka fara tun daga kasar Afganistan ran mutum miliyan nawa aka rasa, a wannan kasa. Idan ka dawo kasashen  Iraqi  da Libya  da Siriya da Yemen da Sudan da Kudancin Sudan da sauran kasashe daban daban na musulmai,  masifu sun fado masu. Kuma duk saboda kauce wa Allah ne, da aka yi.

  Saboda haka Allah madaukakin sarki ya bayyana mana idan irin wannan annoba ta zo, tana gamewa ne ga kowa da kowa, kamar yadda Allah madaukakin sarki yake cewa ku ji tsoron fitina, idan fa ta zo ba za ta shafi wadanda suka jawo ta kawai ba. Za ta hada kowa da kowa ne.

  Saboda haka annoba tana zuwa ne bisa ga abin da hannayenmu na dama ya jawo mana. Don haka wajibi ne mu koma ga Allah mu cigaba da rokonsa.

  A nan Najeriya idan ka lura, wannan cuta ta Korona da ta shigo, mutum daya ne aka ce ya shigo da ita. Kuma yanzu ana nan ana binciken duk mutanen da ya yi mu’amula da su. Saboda haka sai mu roki Allah madaukakin sarki, abin ya tsaya a can wurin.

  Kuma Manzon Allah SAW yana ce mana idan annoba ta shafi gari, kada mutanen da suke cikin garin su fita, haka kuma mutanen da ba sa cikin garin, kada su je su shiga wannan gari. Domin haka musulunci ya tsara. Don haka muke kira ga hukumar Najeriya ta yi la’akari da cewa akwai wasu kasashe da muke mu’amula da su. Kuma an tabbatar cewa wadannan kasashe wannan cuta ta shiga. Don haka mu’amalar da za mu yi da su a dakatar. A kula da filayen jiragenmu da tashoshin jiragen ruwa.

  GTK: To mene ne mafita kan wannan al’amari?

  Sheikh Sulaiman: Mafita  ita ce babu maganar tsoro, amma tsoro irin na al’ada wannan babu laifi. Amma mutum ya ji tsoron mutuwa, mutane su rikice suna tsoro wai kada su mutu. Mutuwa dai ba a sha mata kauda bara, abin da Allah madaukakin sarki yake ce mana ka gaya masu mutuwar da kuke gujewa lallai wannan mutuwa, za ta zo ta same ku. Don haka mutum ya gujewa mutuwa, bata taso ba. Allah madaukakin sarki yana bayyana mana ba zai yiwu ba, ga  wani rai  ya mutu ba, sai idan kwananta ya kare. Saboda haka ban ga dalilin da zai sanya mutane,  su ji tsoron mutuwa ba, domin  kullum muna cikinta.

  Idan kanajin tsoron cutar  Kurona. To ai mu a nan   kullum muna cikin cutar Kurona, tun shekaru 11 da suka gabata.  Tun daga cutar boko haram, wanda a kullum suna kashe mutane,  ga masu kai hare hare ga masu garkuwa da mutane ga ‘yan fashi da makami ga direbobi,  da suke mugun gudu suna hadarurruka.  Mutane suna mutuwa, duk wadannan abubuwa annoba ce.

  Don haka mafita shi ne mu koma ga Allah, mu roke shi ya ye mana wannan annoba. Misali a lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari bashi da lafiya, da musulmin Najeriya da kiristocin Najeriya har da waxanda basu yarda da Allah ba, mun yi ta rokon Allah madaukakin sarki, kan ya bai wa shugaban kasa lafiya  kuma ya amshi addu’armu, ya ba shi lafiya.

  Saboda haka a yanzu ma sai mu tashi mu roki Allah, ya yaye mana wannan annoba. Allah ya ce ku ta rokon gafara, Allah zai gafarta maku zai saukar maku da ruwan sama, zai ba ku dukiya ya ya ba ku ‘ya’ya masu lafiya da biyayya da tarbiya, wannan shi ne mafita.

  GTK: Sakamakon wannan annoba ta Korona kasar Saudiya ta dakatar da al’ummar duniya  zuwa kasar, don gudanar da aikin Umra mene ne za ka ce kan wannan al’amari?

  Sheikh Sulaiman: Gwamnatin Saudiya ta yi hangen nesa kan wannan mataki da ta dauka. Domin idan ka lura duk duniya babu inda ake zuwa a taru, irin kasar Saudiya. Mutanen da suke zuwa Umara Saudiya dai dai suke da  mutanen da suke zuwa aikin hajji. Domin suna zuwa ne daga kasashe daban daban. Don haka idan masu wannan cuta suka shigo kasar, za su hadu da sauran mutanen duniya. Domin za a hadu a masallaci, da wajen cin abinci da wajen shiga  motoci da jiragen sama. Kuma idan aka hadu da masu wannan cuta aka cakudu, kaga zai kasance sun baza wannan cuta kasar ta Saudiya, kuma duk mutanen da suka zo daga sauran  kasashen duniya idan suka koma, kasashensu cutar za ta dada bazuwa.

  Ka ga ashe Saudiya ba wai kasarta kadai ta kare ba. Har  da sauran kasashen duniya ta kare kan wannan mataki da ta dauka. Don haka muna tare da wannan mataki da kasar Saudiya ta dauka, 100 bisa 100 domin shi ne koyarwar Manzon Allah SAW da yake cewa, idan annoba  ta auku a gari, kada abar wadanda suke cikin garin su fita, kuma kada abar wadanda basa cikin garin su shigo. Kowa ya yi hakuri da abin da Allah madaukakin sarki ya dora masa.

  Kuma muna yabawa shugaban hukumar alhazai ta Najeriya kan sanarwar da ya bayar, na dakatar da karvar kudaden masu zuwa Umara. Sakamakon wannan mataki da Saudiya ta dauka, har sai anga yadda al’amarin ya tsaya. Wannan abu da aka yi, ya nuna kamar an yi adalci domin karbar kudaden mutane ba, a san abin da za a yi ba, a je a yi ta juya masu kudadensu bai dace ba, don haka ya kamata a tsaya a yi la’akari, da wannan.

  Kuma muna kira ga gwamnatin Najeriya kan ta dauki irin wannan mataki ta hana shigo da duk wasu kayayyaki daga kasashen da suke fama da wannan annoba, kuma ta hana mutanensu shigowa, kuma a hana ‘yan Najeriya zuwa wadannan kasashe.

   

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here