Dattijuwa ‘Yar Shekaru 70 Ta Jagoranci Mafarauta Shiga Daji Kashe ‘Yan Bindiga 40 A Neja

0
1452

Daga Usman Nasidi.

WATA mata mai shekaru 70, a karshen makon da ya gabata ta jagoranci tawagar ‘yan banga tsirara sun shiga daji sun yi maganin wasu ‘yan bindiga da ke addabar wasu kananan hukumomi a jihar Neja inda suka lashe a ƙalla ‘yan bindiga 40.

Bayan kashe ‘yan bindigan an gano cewa sun kwato manyan makamai daga hannun ‘yan bindigan bayan fafatawa da suka yi a karamar hukumar Zugurma Mashegu a jihar.

An ruwaito cewa jagorar su ‘mace’ ta shafa wa yan bangan wasu magungunan gargajiya a kafarsu kafin ta yi musu jagora suka shiga dajin na Zugurma inda ta ce su yi harbi domin ‘yan bindigan da ke boye a dajin su fito.

Wata majiya ta ce ‘yan bindigan sun fito daga inda suka boye suna harbi amma ba su ga matan ba da ‘yan bangan.

Hakan ya sa mafarautan suka bi sahun ‘yan bindigan inda suka damke aƙalla 40 daga cikinsu yayin da wasu suka tsere.

Wani kwararar majiya daga unguwar ya ce an umurci kwanan ‘yan bindigan da ya boye a kan bishiya ya sako kuma aka kama shi yayin da wasu ‘yan bindigan da suka shiga cikin gari siyo katin waya da wasu kayan masarufi suma an kama su an mika wa yan sanda .

Mafarautan sun shaida wa wasu ‘ yan kauyen cewa ba su kashe shugaban yan bindigan bane saboda suna son ya ba wa ‘yan sanda bayanai kan yadda za a kamo sauran.

Rundunar ‘yan sandan jihar ba ta ce komai a kan lamarin ba yayin da wani babban ɗan sanda ya ce an tura jami’ai su tafi dajin domin bin sahun yan bindigan da nufin kamo sauran.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here