”Mun Yi Amfani Da Kasafin Kudin 2019 Yadda Ya Dace”

  0
  415

  Rabo Haladu Daga Kaduna

  SHUGABAN Karamar  Hukumar”Yankwashi Hon. Dauda Dan_Auwa Karkarna, da ke Jihar Jigawa  ya bayyana irin nasarorin da ya samu ta fuskar yin amfani da kasafin kudin 2019 yadda ya kamata saboda ya samar da gine-ginen sababbin ajujuwa ga daukacin makarantun feramare da ke karamar hukumar tare da yin gyare-gyaren wadanda suka lalace da sama wa dalibai kayan koyan karatu da kujerun zama duk na zamani.

  Hon.Dauda Dan_Auwa Karkarna yayi wannan jawabi ne ga manema labarai a yayin zantawarsu a Karamar Hukumar dake garin “Yankwashi A Jihar Jigawa, yakara dacewa a shugabancinsa ya samar da fanfunan burtsa tse na  tuka-tuka ga daukacin ciki da wajan karamar hukumar tare da gya gyara wadanda suka lalace domin rage matsalar karancin ruwan sha da ake fuskanta a kodayaushe tare da sayo kayayakin aikin Samar da ruwansha na naira million 3 daza a raba ga dukkanin mazabun.

  ‘” Kuma mun raba babura ga matasa 30 domin susami abinyi dan rage zaman banza a karamar hukumar tare da Samar da katafaran dakin kwana na masu yi wa kasa shidima da ake turowa karamar hukumar  saboda susami dakunan kwana batare da samun wata matsala ba.

  Da samar da hanyoyin ruwa tayar da in akayi ruwan  sama zai sami hanyar wucewa da kuma gigina kwalbatoci a duk inda ya kamata.

  Shugaban Karamar hukumar Hon. Dauda Dan_ Auwa Karkarna ya ce kasafin kudin 2020  Za “a yi amfani da shi ta wajen yin sababin tituna da daga darajar asibitin karamar hukumar ya zuwa baban asibiti da za a rinka kwantar da marasa lafiya tare da fadada shi da samar masa kayayakin aiki na zamani da sama wa likitoci dakunan kwana da sauran ma aikatan  asibitin baki daya.

  Yakara dacewa Bayan sun samar da hanyoyi zasu tabbatar da ganin anatsafata ce mahali yadda yakamata tare da samawa matasa aikin yi domin rage zaman banza da kula da aikin gona ta samar da taki da irin shuka da tallafa wa manoma wajan ba su rance..

  Haka Kuma ya ce za su kammala duk wani aiki da ba su kammala ba a shekarar da ta gabata ta 2019.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here